Posts

Showing posts from September 26, 2020

๐˜๐š๐ง๐๐š ๐ฒ๐š๐ง ๐ฆ๐š๐ญ๐š ๐ค๐ž ๐ง๐ž๐ฆ๐š๐ง ๐ฆ๐š๐ณ๐š๐ฃ๐ž๐ง ๐€๐ฎ๐ซ๐ž

Image
   BBC News , Hausa Tsallaka zuwa  ©©๐๐๐‚ ๐ก๐š๐ฎ๐ฌ๐š Yadda mata ke neman mijin 'rufin asiri' ta intanet a Najeriya Duk wani namiji ko mace da ta kai wani munzali na manyance abu na farko da ake yi mata fata shi ne samun miji na gari. Bisa al'adar ฦ™asar Hausa namiji ne yake ganin mace idan hankalinsa ya kwanta da ita sai ya tura iyaye ko manyansa a nema masa izinin har a kai matakin soma batun aure. Ko da yake a wasu lokutan akwai auren haษ—i da iyaye kan yi wa ฦดaฦดansu don ฦ™arfafa zumunci ko abota tsakanin iyalai biyu. Amma kamar yadda Hausawa ke cewa duniya juyi-juyi, kusan a wannan lokaci zamani ya zo da abubuwa da dama inda a wasu lokuta ma mace ke iya ganin namiji ta furta hankalinta ya natsu da shi ko tana fatan ya aure ta. Wani abu kuma da ke sake jan hankali a wannan zamani shi ne yadda ake amfani da kafar sada zumunta ko intanet wajen neman miji ko mata. Baya ga shafukan sada zumunta kamar Facebook da su Twitter da Instagram da wasu kan ce anan suka hadu, ana kum...