'YAN SHI'A A NAJERIYA SUN GUDANAR DA TATTAKI
'Yan shi'a sungudanar da Tattaki a Najeriya. Kamar ko wace shekara 'yan shi'a mabiya El'zakzaky a Najery suna gudanar da Tattaki domin kwatanta irin abinda ya faru ga jikan Annabi (S) sayyadi Husain. 'Yan shi'ar sunbi sahun takwarorin su na sassan duniya da suke takawa a kasa zuwa birnin karbala domin ziyarar sayyadina Husain. A Najeriya 'yan shi'ar suna tashi ne daga bangarori shida zuwa Zariya su karkare tattakin nasu a can kuma suyi addu'a da jawabi daga bakin Sheikh El'zakzaky. Amma tun bayan arangama da aka samu tsakanin su, da sojoji a shekarar 2015 wanda yayi sanadiyyar mabiya malamin 347 a rahoton gwamnatin, da jikkata wasu da dama, gami da kama Sheik El'zakzaky da matarsa, yasa suka janye da zuwa cikin Birnin na Zariya domin kaucewa wata matsalar. Duk da haka a wasu lokutta ana samun kashe kashe daga jami'an tsaro abisa hanyar tasu kafin zuwa inda zasu karkare tattakin kamar a kano da aka taba samun asarar rayuka da dama, sh...