MUHIMMAN ABUBUWA BIYAR DA BUHARI YAYI MAGANA A KANSU-bbc hausa
Nigeria @60: Muhimman abubuwa biyar da Buhari ya ce yayin jawabinsa Sa'o'i 5 da suka wuce ASALIN HOTON, NIGERIA PRESIDENCY A ranar Alhamis, 1 ga watan Oktoban 2020 ne Najeriya ta cika shekara 60 da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka. A safiyar Alhamis ne shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya yi jawabi na musamman ga 'yan ƙasar inda jawabin ya fi mayar da hankali kan haɗin kan ƙasar. Ga wasu daga cikin muhimman batutuwan da shugaban ya taɓo a jawabinsa: Haɗin kai Jigo ko kuma babban saƙo a cikin jawabin shugaban ƙasar shi ne kan batun haɗin kai, domin shugaban a wurare daban-daban ya nuna cewa idan 'yan ƙasar suka haɗa kansu za a samu ci gaba mai ɗorewa. "Idan muka haɗa kanmu za mu iya sauya yadda muke a yanzu domin kawo ci gaba mai amfani a garemu kuma za mu iya taimakon kanmu ƙwarai". Shugaba Buhari ya bayyana cewa ta hanyar haɗin kai ne 'yan Najeriya za su magance ƙalubale daban-daban da suke fuskanta Warkar da Najeriya daga raunin da ta samu...