Posts

Showing posts from October 3, 2020

ƘASAR MASAR TA GANO AKWATIN GAWA DA AKA BINNE TSAWON SHEKARA 2,500

Image
   Masar ta gano akwatinan gawa da aka binne shekara 2,500 AFP Copyright: AFP Masana tarihi a Masar sun ce sun gano akwatunan gawa 59 da aka binne cikin yanayi mai kyau, a makonnin baya-bayan nan. Kamfanin dillacin labarai na AFPya ruwaito cewa daya daga cikin akwatunan da aka bude wanda ya kwashen sama da shekara 2,500 a kasa, masana tarihin sun ce an naɗe wanda ke ciki ne da farin tufafi. Tun bayan gano wasu akwatina 13 da aka yi sati uku baya, ake ci gaba da gano wasu masu yawa a haƙar da ake yi wadda ba ta wuce mita 12 be, kwatankwacin taku 40. AFP Copyright: AFP Za a iya gano wasu akwatunan a binne a ƙasa, in ji ministan kula da harkokin yawon buɗe ido Khaled al-Anani, wanda ya bayyana hakan a kusa da pyramid of Djoser da ya kusa shekara 4,700. Haƙar da ake yi a Saqqara a yan shekarun nan, takai ga samo wasu abubuwa da mutanen baya suka kera da kuma gawawwakin dabbobi irin su maciji tsintsaye da kwari da dai wasu sauran dabbobi. AFP Copyright: AFP Article share tools  View m...