Cutar Corovirus A Iran: "Damuwa Da Talakawan Kasarsu Da Jami'an Gwamnatin Kasar ta Iran Ke Yi Yasa Manyan Jami'an Gwamnatin Kasar Suka Fi Kamuwa da cutar Coronavirus" -Inji Daraktan WHO
An Bayyana Dalilan Da Yasa Manyan Jami'an Gwamnatin Kasar Iran Ke Kamuwa Da Cutar CoronVirus. Daraktar kungiyar lafiya ta duniya (WHO) a gabashin duniya Dr.Rechard Brennan ya bayyana dalilan da yasa manyan Jami'an gwamnatin Kasar Iran ke kamuwa da cutar shake makoshi na Korona Bairus(COVID-19. Daraktan ya bayyana hakan ne a birnin Tehran a lokacin da ya ziyarci Iran,kana ya ziyarci inda ake killace da masu cutar domin ya gane wa idonsa yadda ake kula da lafiyarsu. inda ya yi kira ga kasashen duniya da su yi koyi da kasar ta Iran wajen yakar cutar wannan cuta ta Korona. Dr.Rechard ya kuma bayyana cewar,Iran ta ciri tuta wajen yin yaki da wannan cutar, sannan yayi kira ga kasashen yankin da duniya baki daya da su yi koyi da Iran wajen yakar wannan cutar. Ya kara da cewar,Iran tana da ingantattun kayan aiki na zamani masu kyawun gaske,kuma a yankin Asiya kakaf bai ga kayan aiki irin na Iran din ba. Yace kungiyarsa ta WHO ta bada sharuddan yakar wannan cutar,kuma Iran ...