Posts

Showing posts with the label LABARUN DUNIYA

JIRGIN RUWAN ANNABI NUHU DA AMURIKA TA KERA A SHEKARAR 2018

Image
Amurka 'ta kera jirgin Annabi Nuhu' 2 Nuwamba 2018 Wanda aka sabunta 8 Nuwamba 2018 An sabunta labarin bayan da aka fara wallafa shi ranar 20 ga watan Yulin 2016. ASALIN HOTON, GETTY IMAGES Bayanan hoto, An kashe Dala miliyan 100 wajen gina jirgin Ma'aikatar kirkire-kirkire ta jihar Kentucky ta Amurka, ta kashe tsabar kudi har Dala miliyan 100 wajen gina wani jirgin ruwa kwatankwacin kwamin Annabi Nuhu, bisa dogaro da yadda aka siffanta shi a littafin Injila. Kelly Grovier ya yi nazari kan hakan. Shin da me kake neman tsira a wannan duniyar? Addini? Ko Iyalinka? Ko kuma harkar wasanni? Wasu hotuna da suka rinka kai-komo a kafafen yada labarai da na shafukan sada zumunta, a 'yan kwanakin nan dangane da wani jirgin ruwa da aka gina, sun haddasa wata mahawara a tsakanin mutane a arewacin jihar Kentucky, abin da kuma ya yi nuni da irin yadda al'umma ke neman kariya daga wasu bakin al'adu da ba sa so. Hotunan katafaren jirgin da aka gina domin kwaikwayon kwamin Annab...

BUHARI YA GABATAR WA MAJALISA DA KASAFIN KUDIN SHEKARA 2021

Kasafin Kuɗin Najeriya na 2021: Buhari ya gabatar wa majalisa kasafin naira tiriliyan 13.08 8 Oktoba 2020, 08:27 GMT Buhari ya bukaci 'yan majalisa su amince da kasafin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kuɗin ƙasar kimanin naira tiriliyan 13.08 na shekarar 2021 a gaban Majalisar Dokokin ƙasar - a zaman hadin gwiwa tsakanin majalisar dattawa da ta wakilai. Hasashen kuɗin ya fi na bara da tiriliyan 2.28, inda na baran ya kasance naira tiriliyan 10.805. A yayin da yake gabatar da kuɗin Shugaba Buhari ya ce samun kuɗaɗen shiga don amfani da su wajen kasafin kuɗin shi ne babbar matsalar da gwamnatinsa ke cin karo da shi. Sannan kuma ya ce ministoci za su dinga sa ido don tabatar da cewa hukumomin karɓar kuɗaɗen haraji na ayyukansu yadda ya kamata. Shugaba Buhari ya bayyana ƙudurin kasafin kuɗin da cewa na farfaɗo da tattalin arzikin kasa ne, bisa la'akari da ƙalubalen da Najeriya, kamar sauran kasashen duniya ta fuskanta daga annobar korona, wadda ta durƙusar ...

ƘASAR MASAR TA GANO AKWATIN GAWA DA AKA BINNE TSAWON SHEKARA 2,500

Image
   Masar ta gano akwatinan gawa da aka binne shekara 2,500 AFP Copyright: AFP Masana tarihi a Masar sun ce sun gano akwatunan gawa 59 da aka binne cikin yanayi mai kyau, a makonnin baya-bayan nan. Kamfanin dillacin labarai na AFPya ruwaito cewa daya daga cikin akwatunan da aka bude wanda ya kwashen sama da shekara 2,500 a kasa, masana tarihin sun ce an naɗe wanda ke ciki ne da farin tufafi. Tun bayan gano wasu akwatina 13 da aka yi sati uku baya, ake ci gaba da gano wasu masu yawa a haƙar da ake yi wadda ba ta wuce mita 12 be, kwatankwacin taku 40. AFP Copyright: AFP Za a iya gano wasu akwatunan a binne a ƙasa, in ji ministan kula da harkokin yawon buɗe ido Khaled al-Anani, wanda ya bayyana hakan a kusa da pyramid of Djoser da ya kusa shekara 4,700. Haƙar da ake yi a Saqqara a yan shekarun nan, takai ga samo wasu abubuwa da mutanen baya suka kera da kuma gawawwakin dabbobi irin su maciji tsintsaye da kwari da dai wasu sauran dabbobi. AFP Copyright: AFP Article share tools  View m...

𝐒𝐡𝐮𝐠𝐚𝐛𝐚 𝐁𝐮𝐡𝐚𝐫𝐢 𝐧𝐚 𝐍𝐢𝐣𝐞𝐫𝐢𝐚 𝐲𝐚 𝐟𝐚𝐝𝐢 𝐝𝐚𝐥𝐢𝐥𝐢𝐧 𝐤𝐢𝐧 𝐜𝐢𝐫𝐞𝐰𝐚 𝐌𝐚𝐥𝐢 𝐭𝐚𝐤𝐮𝐧𝐤𝐮𝐦𝐢

Image
   Buhari ya faɗi dalilin ƙin cire wa Mali takunkumi Reuters Copyright: Reuters Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce akwai wasu "batutuwa da ake bukatar warwarewa" a game da shirin sojin Mali na mika mulki ga farar hula kafin kungiyar Ecowas ta cire takunkumin da ta sanya wa kasar. Ecowas ta sanya wa Mali takunkumin ne bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta a watan jiya. Daya daga cikin sharudan janye wa kasar takunkumi shi ne nada shugaba da firaiminista farar hula. Kodayake sojojin sun cika wannan sharadi, shugabansu Kanar Assimi Goita yana ci gaba da zama a matsayin mataimakin shugaban kasa, lamari da har yanzu bai gamsar da Ecowas ba. Ofishin Shugaba Buhari ya fitar da sanarwar cewa watakila shugabannin kasashen Yammacin Afirka za su sake ganawa domin tattaunawa kan rikicin siyasar Mali, bayan ya gana da wakilin Ecowas kuma tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan. "A cewar wakili na musamman, har yanzu shugabannin sojin ba su c...