ƘASAR MASAR TA GANO AKWATIN GAWA DA AKA BINNE TSAWON SHEKARA 2,500

 Masar ta gano akwatinan gawa da aka binne shekara 2,500

AFP

Masana tarihi a Masar sun ce sun gano akwatunan gawa 59 da aka binne cikin yanayi mai kyau, a makonnin baya-bayan nan.

Kamfanin dillacin labarai na AFPya ruwaito cewa daya daga cikin akwatunan da aka bude wanda ya kwashen sama da shekara 2,500 a kasa, masana tarihin sun ce an naɗe wanda ke ciki ne da farin tufafi.

Tun bayan gano wasu akwatina 13 da aka yi sati uku baya, ake ci gaba da gano wasu masu yawa a haƙar da ake yi wadda ba ta wuce mita 12 be, kwatankwacin taku 40.

AFP

Za a iya gano wasu akwatunan a binne a ƙasa, in ji ministan kula da harkokin yawon buɗe ido Khaled al-Anani, wanda ya bayyana hakan a kusa da pyramid of Djoser da ya kusa shekara 4,700.

Haƙar da ake yi a Saqqara a yan shekarun nan, takai ga samo wasu abubuwa da mutanen baya suka kera da kuma gawawwakin dabbobi irin su maciji tsintsaye da kwari da dai wasu sauran dabbobi.

AFP

Comments

Popular posts from this blog

JIRGIN RUWAN ANNABI NUHU DA AMURIKA TA KERA A SHEKARAR 2018

𝐍𝐈𝐆𝐄𝐑𝐈𝐀 @60:𝐌𝐔𝐋𝐊𝐈𝐍 𝐒𝐎𝐉𝐀 𝐌𝐀𝐒𝐔 𝐇𝐀𝐋𝐈𝐍 𝐓𝐒𝐈𝐘𝐀 𝐃𝐀 𝐍𝐀 𝐊𝐈𝐑𝐊𝐈

𝙔𝙖𝙣𝙙𝙖 𝙢𝙖𝙯𝙖𝙣𝙗𝙖𝙩𝙖 𝙠𝙚 𝙩𝙨𝙞𝙣𝙩𝙖𝙧 𝙠𝙬𝙖𝙧𝙤𝙧𝙤𝙣 𝙧𝙤𝙗𝙖 𝙨𝙪𝙣𝙖 𝙨𝙖𝙮𝙚𝙧𝙬𝙖 𝙟𝙖𝙢𝙖 𝙖