Posts

Showing posts from December 31, 2019

RAHOTANNI DAGA BAGHADAD TA KASAR IRAQ

Rahotanni sun bayyana cewa;Jakadan Amurka ya tsere daga Bagagaza sakamakon boren Al'umma. Daga Awwal Isa Musa Bayan ayyana zaman makoki na kwana 3 wanda Firaministan riko na Iraqi Adel Abdul Mahdi yayi,da kuma furucin Allah wadai ga Amurka wanda babbabn marja'in Addini na Iraqi yayi ga Amurka,dubban mutane sun fito zanga-zangar la'anta da kin jinin Amurka a biranen Iraqi da dama. Mutanen da suka yi kwamba suka mamaye ofishin Jakadancin Amurka dake birnin Bagadaza,suna kiran "mutuwa ga Amurka!mutuwa ga Israila!sannan suna kiran da a kamo jakadan a hukunta shi.  Hakan ya tilasta tserewar Jakadar daga ofishinsa dake " Green Zone" zuwa wata mabuya ta daban,abin da har yanzu an ki a bayyana inda jakadan ya buya. An bayyana cewar,an ga wasu da boyayyun fusaku cikin bakaken mota suna tserewa,daga nan aka sanar da ficewar jakadan. Masu zanga-zangar na kira da "Tilas a rufe ofishin jakadancin Amurka dake Baghdad, Iraqi,kuma tilas majilisar kasar tayi do...