Posts

Showing posts with the label TANBIHI

๐’๐ข๐ฒ๐š๐ฌ๐š๐ซ ๐š๐ฌ๐š๐ฅ๐ข๐ง ๐๐š๐ก๐š๐ฎ๐ฌ๐ก๐ž ๐›๐š๐ฆ๐š๐ ๐ฎ๐ฃ๐ž

Image
 ๐’๐ข๐ฒ๐š๐ฌ๐š๐ซ ๐š๐ฌ๐š๐ฅ๐ข๐ง ๐๐š๐ก๐š๐ฎ๐ฌ๐ก๐ž ๐๐š๐ฆ๐š๐ ๐ฎ๐ฃ๐ž:โ„Ž๐‘Ÿ๐‘ก๐‘ฃ๐‘›๐‘’๐‘ก๐‘ค๐‘œ๐‘Ÿ๐‘˜.๐‘›๐‘”@๐‘”๐‘š๐‘Ž๐‘–๐‘™.๐‘๐‘œ๐‘š ๐ท๐‘œ๐‘š๐‘–๐‘› ๐‘Ž๐‘–๐‘˜๐‘œ ๐‘š๐‘Ž๐‘›๐‘Ž ๐‘‘๐‘Ž ๐‘ โ„Ž๐‘Ž๐‘ค๐‘Ž๐‘Ÿ๐‘Ž ๐‘˜๐‘œ ๐‘Ÿ๐‘Žโ„Ž๐‘œ๐‘ก๐‘Ž๐‘›๐‘›๐‘–. Wata shekara, aiki ya kaini wata jiha a cikin jihohin arewa maso gabas. Da yamma sai na fito daga otel ษ—in da aka yi mana masauki, da nufin zagawa inga gari. Ko ba komi, ai Hausawa sun ce na zaune bai ga gari ba. A cikin gari nayi isha'i, sa'annan na fara tattaki da nufin dawowa masauki. A bisa hanya na hango wani shagon abinci irin wanda Turawa ke kira restaurant. Sai na faษ—a da nufin yin ฦ™oto. Bayan na zauna, an kawo mani irin abincin da na buฦ™ata har na fara ci, sa'annan ne na ankara da hirar da wasu matasa suke yi a wani teburin da ke cikin ษ—akin abincin. Matashi na Farko: Kakana, wanda ya daษ—e a cikin hausawa, shine ya ke tabbatar mani da cewa babu wasu mutane da ake kira hausawa. Duk wanda kaji ance bahaushe ne, to in ka bincika yana da asali a wata ฦ™abilar cikin kakanninsa. Matashi na Biyu:...

๐๐ˆ๐†๐„๐‘๐ˆ๐€ @60:๐Œ๐”๐‹๐Š๐ˆ๐ ๐’๐Ž๐‰๐€ ๐Œ๐€๐’๐” ๐‡๐€๐‹๐ˆ๐ ๐“๐’๐ˆ๐˜๐€ ๐ƒ๐€ ๐๐€ ๐Š๐ˆ๐‘๐Š๐ˆ

Image
  BBC News , Hausa Tsallaka zuwa abubuwan da ke ciki Sassa Labaran Duniya Wasanni Nishadi Cikakkun Rahotanni Bidiyo Shirye-shirye na Musamman Shirye-shiryen rediyo Nigeria @60: 'Mulkin soja, masu halin tsiya da na kirki' Mintuna 29 da suka wuce Daga Mahmud Jega, mai sharhi kan al'amura a Najeriya ASALIN HOTON, GETTY IMAGES Bayanan hoto, Janar Yakubu Gowon ya mulki Najeriya daga shekarar 1966 zuwa 1975 ฦณan Najeriyar da ke ฦ™asa da shekaru 30, waษ—anda kuma su ne suka fi yawa yanzu a cikin al'umma -- ba su san mene ne mulkin soja ba. A yanzu Najeriya na cikin shekararta ta 21 na ษ—orarren mulkin dimokraษ—iyya ba tare da sauyi ba, wanda shi ne mafi tsayi da aka taษ“a gani tun bayan samun ฦดancin kan ฦ™asar. Jamhuriyya ta farko, wacce Sir Abubakar Tafawa Balewa ya yi mulki a matsayin Fira Minista sannan Dr. Nnamdi Azikiwe ya kasance shugaban ฦ™asar, ba ta yi nisan kwana ba, shekara biyar kawai ta ษ—auka, daga watan Oktoban 1960 zuwa Oktoban 1966. Ko da kuwa mun fara lissafi ne daga...