๐๐ข๐ฒ๐๐ฌ๐๐ซ ๐๐ฌ๐๐ฅ๐ข๐ง ๐๐๐ก๐๐ฎ๐ฌ๐ก๐ ๐๐๐ฆ๐๐ ๐ฎ๐ฃ๐
๐๐ข๐ฒ๐๐ฌ๐๐ซ ๐๐ฌ๐๐ฅ๐ข๐ง ๐๐๐ก๐๐ฎ๐ฌ๐ก๐ ๐๐๐ฆ๐๐ ๐ฎ๐ฃ๐:โ๐๐ก๐ฃ๐๐๐ก๐ค๐๐๐.๐๐@๐๐๐๐๐.๐๐๐๐ท๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐ ๐ โ๐๐ค๐๐๐ ๐๐ ๐๐โ๐๐ก๐๐๐๐.
Wata shekara, aiki ya kaini wata jiha a cikin jihohin arewa maso gabas. Da yamma sai na fito daga otel ษin da aka yi mana masauki, da nufin zagawa inga gari. Ko ba komi, ai Hausawa sun ce na zaune bai ga gari ba.
A cikin gari nayi isha'i, sa'annan na fara tattaki da nufin dawowa masauki. A bisa hanya na hango wani shagon abinci irin wanda Turawa ke kira restaurant. Sai na faษa da nufin yin ฦoto.
Bayan na zauna, an kawo mani irin abincin da na buฦata har na fara ci, sa'annan ne na ankara da hirar da wasu matasa suke yi a wani teburin da ke cikin ษakin abincin.
Matashi na Farko: Kakana, wanda ya daษe a cikin hausawa, shine ya ke tabbatar mani da cewa babu wasu mutane da ake kira hausawa. Duk wanda kaji ance bahaushe ne, to in ka bincika yana da asali a wata ฦabilar cikin kakanninsa.
Matashi na Biyu: Na yarda da wannan maganar. Kasan a ABU Zaria nayi karatu. Wallahi duk hausawan da na sani, in muna hira dasu zakaji sunce kakaninsu filanine ko barebari ko wata ฦabilar. Amma bahaushe usul ban taษa gani ba.
Matashi na Farko: (bayan yayi wata yar gajerar dariya). Ai shi wannan kakan nawa ya gaya mani cewa duk wanda kaji yace maka shi bahaushe ne usul, to ka tabbata baya da asali
Jin inda hirar su tasa gaba, sai nayi abin da ba kasafai nakeyi ba, shiga sharo ba shanu. Sai na ษauki kwanon abinci na, da gorar ruwan da aka kawo mani, na koma teburin su, nayi masu sallama suka amsa.
"Kuyi haฦuri, naji hirar da kuke yi, 'and I can't resist the urge to join the discussion'. Da farko dai inayi maku albishir cewa ni bahaushe ne na asali. Tunda baku taษa ganin bahaushen asali da baida sofane ba, to ga guda kusa daku, kuna iya taษani kuji, in kunso ma kuna iya ษaukar hoto dani ku ajiye don wata rana in ana muhawarar samuwar asalin bahaushe ku nuna" (mukayi dariya mu duka).
Daga nan na tambaye su, me suka fahimta da kalmar Hausa, suka ce Hausa yare ce kamar turanci dss.
Daga nan sai nayi masu ฦarin bayani kamar haka:
Kalmar Hausa na nufin abubuwa da dama, muhimmai daga ciki sune wadannan guda ukun:
1. Hausa na nufin ฦasar Hausa
2. Hausa na nufin Hausawa watau asalin Hausawa da mutanen ฦasar Hausa.
3. Hausa na nufin harshen Hausa.
Yanzu kuna ganin zai yiwu a samu ฦasar Hausa, a samu harshen Hausa amma ace babu asalin mutanen dake zaune a wannan ฦasar kuma suke amfani da wannan harshen? Kamar fa ace kaje ฦasar larabawa ko Ingila ne, ka samu harshen Larabci ko Ingilishi, amma ace babu mutanen da za'a kira asalin Larabawa ko Turawan Ingilishi.
Don kawai ansamu mutane da yawa a duniya waษanda ba larabawa ko turawa ba suna magana da harshen Larabci ko Turanci, ba zai kore samuwar mutanen da asalinsu Larabawa da Turawa bane.
Daga nan sai Matashi na Farko yace "watau dai kana nufin kai asalin ka bamaguje ne kenan. Don munsan asalin bahaushe bamaguje" (dukkanmu mukayi dariya).
Na sake murmusawa sannan nace "bari in tambayeku, shin kalmar 'Bamaguje' asalin kalmar Larabci ce ko Ingilishi ko Fillanci ko Barbarci ko Nufanci ko wane yare?". Suka yarda cewa kalmar Hausa ce. Daga nan na tambaye su "a bisa adalci, in kun yarda asalin kalmar Hausa ce, wa yafi cancanta ya faษi ma'anar ta fiye da bahaushe?" Suka yarda cewa mai harshe shi yafi cancanta ya fassara ma'anar kalmar sa.
Daga nan sai nayi masu jawabi:
Bamaguje na nufin bahaushen da ba musulmi ba. Nasan babu wani mahalukin da ke shakka ko kokwanto cewa kalmar bamaguje na nufin bahaushen da ba musulmi ba. Tunda hakane, meyasa duk sadda mutum yace asalin sa bahaushe, sai ace masa asalin sa bahaushe ne wanda ba musulmi ba, kuma tunda asalinsa ba musulmi bane baya da asali ko hurumin kiran kansa bahaushe?
Wace ฦabila ce a duniyar nan zata bugi ฦirjin cewa ita asalin ta musulma ce ba kafira ba?
Ko ฦabilar ฦuraishawa da Annabi Muhammadu SAW ya fito a cikin su, kuma aka saukar da ฦur'ani cikin harshen su, kafirai ne masu bautar gumaka kafin zuwan Musulunci. Muna da labarin manyan kafirai ฦuraishawa irinsu Abujahal da Abulahabi. Muna kuma da labarin gaggan gumakan ฦuraishawa irinsu Lata da Uzza. Meyasa in mutum yace shi Balarabe ne, ba'a cewa asalin sa Kafiri ne?
Ina son kuyi nazari.
Meyasa in mutum yace asalinsa babarbare ne, ko bafillace, ko buzu ko banufe ko margi dss, ba'a cewa ashe asalin ka kafiri ne ba musulmi ba? Meyasa sai in Bahaushe ne in ya faษi asalinsa ake tunatar da shi cewa asalin sa ba musulmi bane?
Akwai dalili, ga kuma dalilin
Tun bayan jihadin Shehu Usmanu Danfodiyo da ya jaddada addinin Musulunci a ฦasar Hausa, harshen Hausa ya samu ษaukaka a tsakanin tsararrakin sa a wannan nahiya tamu. Masu amfani da harshen suka ฦaru ninkin ba ninkin, har harshen ya samu ฦarษuwa a cikin duniya.
Wasu mutane da suke hassada da ฦyashin wannan ษaukaka da harshen Hausa ya samu, sune suka kitsa makircin jifan duk wanda yayi ikirarin cewa asalinsa bahaushe ne da kalmar maguzanci. Kun san dalili? Strategy ne na ayi discouraging Hausawa daga amsa cewa asalin su Hausawa ne don gudun kada a kira su maguzawa. Ta haka sai a wayi gari babu mai iya fitowa fili yace shi bahaushe ne!
Da mutum yace shi bahaushe ne, sai ace masa indai baya da asali a wata ฦabilar tabbas asalinsa bamaguje ne. Daga nan sai Hausawa su fara gudun alaฦanta asalin su da Hausa don gudun jifa da kalmar maguzanci.Ta haka ake son cimma kore samuwar asalin Hausawa a doron ฦasa, saboda ansawa asalin Hausawan tsoron kiran kansu Hausawa. Kaga daga nan sai ace ga ฦasa da harshe amma babu asalin masu harshen balle su rinฦa tinฦaho.
Wannan makircin na masu hassada ga Hausa ya na tasiri a tsakanin Hausawa. Sau da yawa zaka ga bahaushe yana zaune a matsayinsa na bahaushe kaka da kakanni, da ya tsinto wata tatsuniya da ta danganta shi da wani asali a wajen Hausa sai kaji yana shela "yau na gano ashe asalin mu daga birnin Santanbul muke, kakanmu na kaza ne yazo ฦasar Hausa, muma asalin mu ba maguzawa bane Larabawa ne!
A ฦarshe, ya kai Bahaushe, inason ka sani cewa duk sadda kace asalin ka bahaushe, wani bagwari yace maka ashe asalin ka bamaguje, to so yake ya raina maka wayo da hankali.
Aliyu Ammani
U/Shanu Kaduna
29/09/20
ฦarin bayani: Hoton dake jikin wannan rubutu, hoton Husumiyar Gobarau ce tamu ta Katsina wadda aka gina a matsayin Babban Masallacin Birnin Katsina shekaru sama da 400 kafin Jihadin Mujaddadi Shehu Usmanu Danfodiyo.
Comments
Post a Comment