๐พ๐จ๐ป๐จ ๐ฉ๐จ๐ฉ๐ฉ๐จ๐น ๐ฒ๐ถ๐ป๐ผ ๐ซ๐จ ๐ฒ๐ฌ ๐ฒ๐จ๐ซ๐ผ๐ต๐จ ๐ป๐จ๐ฉ๐จ ๐ผ๐ด๐จ๐น๐ต๐ฐ๐ต ๐จ๐ช๐ฐ ๐ฎ๐จ๐ฉ๐จ ๐ซ๐จ ๐บ๐ฏ๐จ๐น๐ฐ'๐จ๐น ๐บ๐ฏ๐ผ๐ฎ๐จ๐ฉ๐จ๐ต '๐๐จ๐ต ๐บ๐ฏ๐ฐ'๐จ ๐ฐ๐ฉ๐น๐จ๐ฏ๐ฐ๐ด ๐ฌ๐ณ๐๐จ๐ฒ๐๐จ๐ฒ๐
Kotu ta umarci a ci gaba da shari’ar Ibrahim Zakzaky
Wata babbar kotu a Kaduna da ke arewacin Najeriya ta umarci a ci gaba da shari’ar da aka kawo gabanta kan jagoran mabiya Shi’a a kasar, Sheik Ibrahim Zakzaky.
Sheikh Zakzaky da matarsa Zeenatu na rike tun a shekara ta 2015 bayan mutuwar mabiyan sama da 300 a wata arangama da jami’an tsaro a garin Zaria.
Sojoji sun ce sun bude wa mabiyan wuta ne a matsayin martani bayan sun yi kokarin kai wa ayarin motocin babban hafsan sojin kasar hari.
A shekara ta 2019 aka haramta kungiyar bayan shafe tsawon watanni na zanga-zanga da rikici da jami’an tsaro
Lauyan Zakzaky, Mr Femi Falana ya bukaci kotun tayi watsi da tuhumar da ake wa shugaban ‘yan shi’ar.
Sai dai alkali kotun ya ce hakan ba mai yiwuwa ba ne saboda bai gama sauraron gundarin karar da aka shigar ba balantana ya yanke hukunci.
Sannan Elzakzaky bai amsa tuhume-tuhumen da ake masa ba.
Elzakzaky da matarsa sun musanta zarge-zargen da ake musu.
Alkalin dai ya tsayar da Nuwamba a matsayin watan ci gaba da sauraron karar.๐ฒ๐๐๐ ๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐ ๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐ ๐ผ๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐ ๐ ๐ ๐๐๐๐๐'๐๐ ๐ฌ๐๐๐๐๐๐๐๐
Comments
Post a Comment