'๐๐๐ง ๐ฌ๐๐ง๐๐ ๐ฌ๐ฎ๐ง ๐ก๐๐ซ๐๐ ๐ฆ๐๐ข ๐ณ๐๐ง๐ ๐ ๐ณ๐๐ง๐ ๐ ๐ก๐๐ซ ๐ฅ๐๐ก๐ข๐ซ๐ ๐ ๐ฃ๐ข๐ก๐๐ซ ๐ค๐๐ญ๐ฌ๐ข๐ง๐.
Kashe-kashe: Ana zargin ‘Yan Sanda da kashe mai zanga-zanga a Jihar Katsina.
๐ซ๐๐๐๐ ๐จ๐๐๐๐๐๐๐ ๐ ๐ ๐๐๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐ ๐ ๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐ ๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐
Mutanen Garin Jibiya sun fita zanga-zanga a kan kashe-kashen da ake ta yi.
Mazauna garin sun ce an yi kwana da kwanaki ana kai masu hari a Katsina - Tun ba yau ba, ana ta fama da matsalar rashin tsaro a Jihar Shugaban kasar An rasa mutum daya daga cikin mazauna garin Jibiya da su ka shirya zanga-zangar
a sanadiyyar matsalar rashin tsaro da ke addabar yankin na jihar Katsina.
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a jiya cewa al’ummar Jibiya sun yi zanga-zanga domin nuna rashin jin dadin abin da ke faruwa na yawaitar kashe-kashe.
Wajen wannan zanga-zanga, an harbe wani mutumi, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
Rahotanni sun ce, jami'an tsaro sun kama mutane akalla 43 a jiyan Ana zargin dakarun ‘yan sandan Najeriya da aka tura su lafar da wannan zanga-zanga ne su ka harbi wannan Bawan Allah a ranar Litinin, 28 ga Satumba, 2020.
‘Danuwan marigayin wanda ya bayyana sunansa da Abdulhadi, ya yi magana da ‘yan jarida yayin da ya ke kuka, ya ce ‘yan sanda sun kashe masa ‘dan'uwa. “Kanina ne, an kashe shi.” Inji Abdulhadi.
Wani mutumi da ya fito daga kauyen Daddara, mai suna Falalu Abba, ya bayyana cewa dole ta sa talakawan yankin su ka fita zanga-zanga domin nuna bacin ransu. "A ranar Lahadi, kwana 39 kenan a jere, kullum sai an kai hari. Idan aka kira jami’an tsaro, sai su ki zuwa mutane sun gaji don haka su ka fito zanga zangar lumana don nunawa duniya halin da suke ciki"
Comments
Post a Comment