๐๐ข๐ณ๐ถ๐ฎ๐ข๐ณ ๐๐ข๐ฏ๐บ๐ธ๐ฐ๐ฐ๐ฅ ๐ฉ๐ข๐ญ๐ช๐ฎ๐ข ๐บ๐ถ๐ด๐ถ๐ง ๐ต๐ข๐ฏ๐ข ๐ฎ๐ข๐ต๐ถ๐ฌ๐ข๐ณ ๐ด๐ข๐ฏ๐บ๐ข๐ฏ๐ช ๐ฏ๐ช๐ด๐ฉ๐ข๐ฅ๐ช- ๐๐ฆ๐ฎ๐ช ๐ง๐ข๐ฏ๐ช ๐ฌ๐ข๐บ๐ฐ๐ฅ๐ฆ
Halima Yusuf: Jarumar Kannywood na matuฦar kwantar min da hankali – Femi Fani-Kayode
Tsohon ministan zirga-zirgar jiragen sama na Najeriya Femi Fani Kayode ya ce jarumar Kannywood Halima Yusuf na matuฦar kwantar masa da hankali.
Ya kuma musanta cewa zai saki matarsa kana ya auri ita jarumar da cewa duka jita-jita ce maras tushe.
Mr Fani-Kayode ya kuma ce jarumar wacce ake ta rade-radin matar da zan aura ce "aminiyata ce wacce nake matuฦar mutuntawa da ganin ฦimar ta."
Karshen labarin da aka sa a Instagram, 1
"Ana yada jita-jita a shafukan sada zumunta cewa ina shirin sake sakar matata. Hakan ฦarya ne. Miss Halima Yusuf, wacce aka ce budurwata ce, ฦawata ce kuma makusanciyata wacce nake matuฦar girmamawa," in ji shi.
Ya kara da cewa: "Ita da wasu irinta, sun kasance cikin mutanen da suke matuฦar kwantar mini da hankali kuma ina matuฦar godiya a gare ta."
Tsohon ministan ya buฦaci mutanen da ke watsa jitar-jita kan batun su daina.
Yawan jawo ce-ce-ku-ce
Karshen labarin da aka sa a Instagram, 2
Femi Fani-Kayode mutum ne mai yawan yawo ce-ce-ku-ce a kafafen watsa labarai, inda na baya bayan nan ma sai da ya tayar da ฦura bayan da ya ci zarafin wani ษan jaridar Daily Trust a Najeriya.
A cikin watan Agustan wannan shekarar ne dai wani faifen bidiyo da ya mamaye shafukan sada zumunta ya nuna tsohon ministan yana ta zagin ษan jaridar, Eyo Charles.
Dan jaridar dai ya yi masa wata tambaya da ya yi masa da ba ta yi masa daษi ba, a lokacin wata hira da 'yan jarida a birnin Calaba na Jihar Cross Rivers da ke Kudancin Najeriyar.
Har ila yau a watan Yulin shekarar nan ma sai da sarautar gargajiyar da Sarkin Shinkafi Alhaji Mumammadu Makwashe ya bai wa tsohon ministan ta tayar da ฦura.
Sarautar "Sadaukin Shinkafi" da masarautar Shinkafin ta ba shi ta janyo ce-ce-ku-ce a ciki da wajen masarautar, inda wasu daga cikin masu riฦe da muฦaman gargajiya suka ajiye muฦaman nasu.
Femi Fani-Kayode dai ya shahara wajen yin kakkausar suka ga duk abin da ya shafi arewacin Najeriya da kuma Hausawa.
Kalamansa kan kabilun Hausawa da Fulani sun sha tayar da ฦura a ฦasar musamman ma a shafukan sada zumunta.
Comments
Post a Comment