Posts

Showing posts from December 29, 2019

DANGANTAKAR DAUKAR NAUYIN FILMS DA ISAR DA SAKO

Dangantakar Daukar Nauyin Shirya Fim Da Isar Sa'ko? A wannan zamani fim ya Zama tamkar Hantsi leka Gidan Kowa, da wuya ka sami wani mutum daya wanda bashi da alaka da fim ko da kuwa ta kallo ce. Wani sanannen abu kuma shi ne kadan ne daga cikin mutane masu kallon Fim suke da masaniya akan dalilin da yasa ake shirya fim har ya zo gare su su kalla. A fiye da shekaru 100 da suka gabata zuwa yau Fim ya shiga jerin Hanyoyin isar da sako mafi sauri da kuma saukin fahimta. Wannan dalilin yasa 'yan mulki mallaka suka rungumi wannan hanya ta fim wajen yada manufofinsu ga sauran Al'umma. Wasu al'ummun ba su yi fargar jaji ba sun lura da wuri irin barnar da Fim din Turawa ya soma haifarwa a cikin Al'ummar su musamman ga matasa, ganin haka sai suma suka soma shirya fim domin kare kai. Duk Wanda ya Kalli Fima-Fimai na Indiya a Farkon al'amarin Fim din su zaka ga ba komai a ciki sai yada al'adunsu,  sun yi hakan ne kuwa domin mayar da martani ga harin da 'yan mu...