Amurika na neman diyyar Dala biliyan daya da rabi wajen Iran.
Wata sabuwa inji yan caca' Amurka na neman diyar Dala biliyan daya da rabi daga wajen Iran. Wata kotu a Amurka ta yanke wani hukunci mai kama da almara cewar Iran zata biya iyalan tsohon dan leken asirin FBI Mr.Robert Livinson dalar Amurka kimanin $1.4bl sakamakon batar dabon da dan kwangilar yayi yayin wata ziyarar da ya kai zuwa wani tsibiri a cikin Iran din a shekarar 3/2007. Da farko Amurka ta shigar da karar Iran ga MDD,daga baya kuma kasar Swiss ta shiga tsakani domin samo bakin zaren sasantawa ta fuskacin diflomasiyya. - Ana hakan ne katsam,a farkon wannan shekarar ta 2020 sai iyalan Mr.Livinson suka bayyana cewar basu da ragowar sauran fata game da mahaifin nasu,sun tabbatar da cewar,bayanan sirrin da suka samu ya tabbatar musu da rasuwar uban nasu a hannun Iran. Don haka suna neman gwamnatin Amurka da ta nema musu hakkin su daga wuyan Iran. - Sai kuma ga wata kotun Gunduma (District Court) ta yanke hukuncin cewar,bisa wasu kwararan dalilan da ta samu daga iyalan Mr.Livinso...