Skip to main content

MUHIMMAN ABUBUWA BIYAR DA BUHARI YAYI MAGANA A KANSU-bbc hausa

Nigeria @60: Muhimman abubuwa biyar da Buhari ya ce yayin jawabinsa

..

A ranar Alhamis, 1 ga watan Oktoban 2020 ne Najeriya ta cika shekara 60 da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka.

A safiyar Alhamis ne shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya yi jawabi na musamman ga 'yan ƙasar inda jawabin ya fi mayar da hankali kan haɗin kan ƙasar.

Ga wasu daga cikin muhimman batutuwan da shugaban ya taɓo a jawabinsa:

Haɗin kai

Jigo ko kuma babban saƙo a cikin jawabin shugaban ƙasar shi ne kan batun haɗin kai, domin shugaban a wurare daban-daban ya nuna cewa idan 'yan ƙasar suka haɗa kansu za a samu ci gaba mai ɗorewa.

"Idan muka haɗa kanmu za mu iya sauya yadda muke a yanzu domin kawo ci gaba mai amfani a garemu kuma za mu iya taimakon kanmu ƙwarai".

Shugaba Buhari ya bayyana cewa ta hanyar haɗin kai ne 'yan Najeriya za su magance ƙalubale daban-daban da suke fuskanta

Warkar da Najeriya daga raunin da ta samu

Shugaba Buhari ya bayyana cewa wannan wata dama ce da 'yan Najeriya za su gyara ƙasar su. A cewarsa, ya kamata mutane su kawo ƙarshen irin tunanin da suke da shi wanda bai ciyar da ƙasar gaba.

Ya ce bai kamata 'yan ƙasar na nuna wariya irin ta ƙabilanci ba ta yadda ake nuna cewa wani ya fito daga wani yanki na daban.

Ya ce ya kamata 'yan ƙasar su rinƙa ɗaukar kansu a matsayin ɗaya.

Ya ce domin fara warkar da irin wannan raunin, ya kamata 'yan ƙasar su fara kallon kansu a matsayin tsintsiya maɗaurinki ɗaya.

..

Tattalin arziƙi

A jawabin shugaban, ya bayyana cewa yana sane da cewa tattalin arziƙin Najeriya na cikin wani hali kamar yadda na sauran ƙasashen duniya yake.

Ya bayyana cewa ya yi alƙawarin taimaka wa ƙasar wajen cimma burinta na zama ɗaya daga cikin ƙasashe 20 mafi ƙarfin tattalin arziƙi a duniya.

Shugaban ya kuma sake jadda aniyarsa ta cire 'yan Najeriya miliyan 100 daga talauci cikin shekara 10.

Harkar zaɓe

Shugaba Najeriya Muhammadu Buhari ya ce hali irin na ɗan adam ne ke kawo akasarin matsalolin da ake fuskanta a lokacin zaɓe sakamakon yadda mutane ke son samun mulki ta kowane hali.

Shugaban ya jaddada aniyarsa ta samar da zaɓen gaskiya da adalci inda kuma ya bayar da misali da zaɓen jihar Edo da aka kammala a watan jiya.

Ya ce ya kamata zaɓen Edo ya ba 'yan ƙasar ƙwarin gwiwar cewa a shirye yake ya samar da hanyoyi da yanayin tabbatar da ƙuri'ar kowane ɗan Najeriya ba ta yi ciwon kai ba.

Man fetur

A jawabin Shugaban, ya ce ba abin da hankali zai ɗauka bane a ce Najeriya na sayar da man fetir a farashi ƙasa da abin da ake sayarwa a ƙasashen makwafta.

Shugaban ya ce dole ne a sauya farashin man fetir. Ya ce a yanzu ana sayar da kowace lita ɗaya 161, kuma ya bayar da misali da yadda sauran ƙasashe suke sayarwa kamar haka:

  • Chadi na sayar da kowace lita naira 362 a kowace lita
  • Jamhuriyyar Nijar kuma na sayarwa kan naira 346 kan kowace lita
  • Ghana na sayar da kowace lita kan naira 326
  • Sai kuma Masar na sayar da kowace lita kan naira 211 sai kuma Saudiyya 168.

Comments

Popular posts from this blog

JIRGIN RUWAN ANNABI NUHU DA AMURIKA TA KERA A SHEKARAR 2018

𝐍𝐈𝐆𝐄𝐑𝐈𝐀 @60:𝐌𝐔𝐋𝐊𝐈𝐍 𝐒𝐎𝐉𝐀 𝐌𝐀𝐒𝐔 𝐇𝐀𝐋𝐈𝐍 𝐓𝐒𝐈𝐘𝐀 𝐃𝐀 𝐍𝐀 𝐊𝐈𝐑𝐊𝐈

𝙔𝙖𝙣𝙙𝙖 𝙢𝙖𝙯𝙖𝙣𝙗𝙖𝙩𝙖 𝙠𝙚 𝙩𝙨𝙞𝙣𝙩𝙖𝙧 𝙠𝙬𝙖𝙧𝙤𝙧𝙤𝙣 𝙧𝙤𝙗𝙖 𝙨𝙪𝙣𝙖 𝙨𝙖𝙮𝙚𝙧𝙬𝙖 𝙟𝙖𝙢𝙖 𝙖