Posts

Showing posts from October 8, 2020

JIRGIN RUWAN ANNABI NUHU DA AMURIKA TA KERA A SHEKARAR 2018

Image
Amurka 'ta kera jirgin Annabi Nuhu' 2 Nuwamba 2018 Wanda aka sabunta 8 Nuwamba 2018 An sabunta labarin bayan da aka fara wallafa shi ranar 20 ga watan Yulin 2016. ASALIN HOTON, GETTY IMAGES Bayanan hoto, An kashe Dala miliyan 100 wajen gina jirgin Ma'aikatar kirkire-kirkire ta jihar Kentucky ta Amurka, ta kashe tsabar kudi har Dala miliyan 100 wajen gina wani jirgin ruwa kwatankwacin kwamin Annabi Nuhu, bisa dogaro da yadda aka siffanta shi a littafin Injila. Kelly Grovier ya yi nazari kan hakan. Shin da me kake neman tsira a wannan duniyar? Addini? Ko Iyalinka? Ko kuma harkar wasanni? Wasu hotuna da suka rinka kai-komo a kafafen yada labarai da na shafukan sada zumunta, a 'yan kwanakin nan dangane da wani jirgin ruwa da aka gina, sun haddasa wata mahawara a tsakanin mutane a arewacin jihar Kentucky, abin da kuma ya yi nuni da irin yadda al'umma ke neman kariya daga wasu bakin al'adu da ba sa so. Hotunan katafaren jirgin da aka gina domin kwaikwayon kwamin Annab...

BUHARI YA GABATAR WA MAJALISA DA KASAFIN KUDIN SHEKARA 2021

Kasafin Kuɗin Najeriya na 2021: Buhari ya gabatar wa majalisa kasafin naira tiriliyan 13.08 8 Oktoba 2020, 08:27 GMT Buhari ya bukaci 'yan majalisa su amince da kasafin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kuɗin ƙasar kimanin naira tiriliyan 13.08 na shekarar 2021 a gaban Majalisar Dokokin ƙasar - a zaman hadin gwiwa tsakanin majalisar dattawa da ta wakilai. Hasashen kuɗin ya fi na bara da tiriliyan 2.28, inda na baran ya kasance naira tiriliyan 10.805. A yayin da yake gabatar da kuɗin Shugaba Buhari ya ce samun kuɗaɗen shiga don amfani da su wajen kasafin kuɗin shi ne babbar matsalar da gwamnatinsa ke cin karo da shi. Sannan kuma ya ce ministoci za su dinga sa ido don tabatar da cewa hukumomin karɓar kuɗaɗen haraji na ayyukansu yadda ya kamata. Shugaba Buhari ya bayyana ƙudurin kasafin kuɗin da cewa na farfaɗo da tattalin arzikin kasa ne, bisa la'akari da ƙalubalen da Najeriya, kamar sauran kasashen duniya ta fuskanta daga annobar korona, wadda ta durƙusar ...