BUHARI YA GABATAR WA MAJALISA DA KASAFIN KUDIN SHEKARA 2021



Buhari ya bukaci 'yan majalisa su amince da kasafin
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kuɗin ƙasar
kimanin naira tiriliyan 13.08 na shekarar 2021 a gaban Majalisar Dokokin ƙasar
- a zaman hadin gwiwa tsakanin majalisar dattawa da ta wakilai.

Hasashen kuɗin ya fi na bara da tiriliyan 2.28, inda na baran ya kasance naira
tiriliyan 10.805.

A yayin da yake gabatar da kuɗin Shugaba Buhari ya ce samun kuɗaɗen shiga
don amfani da su wajen kasafin kuɗin shi ne babbar matsalar da gwamnatinsa
ke cin karo da shi.

Sannan kuma ya ce ministoci za su dinga sa ido don tabatar da cewa
hukumomin karɓar kuɗaɗen haraji na ayyukansu yadda ya kamata.

Shugaba Buhari ya bayyana ƙudurin kasafin kuɗin da cewa na farfaɗo da tattalin
arzikin kasa ne, bisa la'akari da ƙalubalen da Najeriya, kamar sauran kasashen
duniya ta fuskanta daga annobar korona, wadda ta durƙusar da tattalin arziki ta
ɓangarorin rayuwa daban-daban.

Kuma wannan ya sa gwamnati ta zurfafa tunani wajen tsara hanyoyin raya
tattalin arzikin da kasafin kuɗin da ake sa ran zai ci mukuɗan kudaɗe.

Me kasafin zai mayar da hankali a kai?

Shugaba Buhari ya bayyana ƙudurin kasafin kuɗin da cewa na farfaɗo da tattalin
arzikin kasa ne, bisa la'akari da ƙalubalen da Najeriya, kamar sauran kasashen
duniya ta fuskanta daga annobar korona, wadda ta durƙusar da tattalin arziki ta
ɓangarorin rayuwa daban-daban.

Kuma wannan ya sa gwamnati ta zurfafa tunani wajen tsara hanyoyin raya
tattalin arzikin da kasafin kuɗin da ake sa ran zai ci mukuɗan kudaɗe.

Ana jimullar kuɗin da gwamnatin tarayya za ta kashe a shekara mai zuwa da ya
kai naira tiriliyan goma sha uku, da miliyon dari takwas, wanda ya hada da naira
tiriliyin biyar da naira biliyan sittin da biyar da za a kashe a kan harkokin
gudanarwa na yau da kullum.

Da albashin ma'aikata da ya ki naira tiriliyon uku da biliyon saba'in da shida, da
kuma naira tiriliyan uku da biliyon goma sha biyu na ɗawainiyar biyan bashi.
Wasu hidimomin da za su lashe biliyoyin naira, ciki har da biyan kudin fansho da
sauran wajiban da suka rataya ga wuyan gwamnati.

Shugaban Najeriyar ya bayyana cewa an tsara kudurin kasafin kudin ne ta hanyar
ƙeƙe-da-ƙeƙe, wato sai da aka lura da samun gwamnati ta fuskar kudin-shiga, da
rance ko bashin da za ta ciwo da kuma tallafin da za ta yi, ko wanda zai shiga
hannunta.

Kuma wannan ne ma ya sa gwamnati ta ƙiyasta farashin gangar mai a kan dala
40.

Shugaba Buhari ya jaddada cewa gwamnati ta duƙufa wajen fitar da 'yan
Najeriya miliyan 100 daga ƙangin talauci nan da shekara 10 masu zuwa.

Me ya faru a majalisar?

Ya gabatar da kasafin ne da misalin ƙarfe 11 na safiyar Alhamis.

Rahotanni sun ce an jibge jami'an tsaro da yawa a harabar Majalisar Dokokin da
ke Abuja, inda Shugaba Buharin ya gabatar.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa cikin jami'an tsaron da aka kai har da na hukumar
tsaro ta farin kaya da ƴan sanda da na hukumar hukumar tsaron farin kaya da
kare al'umma wato Civil Defense da na hukumar kare afkuwar haɗura.
Sannan an rage yawan masu shiga cikin majalisar.

An yi zaman majalisar lafiya-lafiya ba tare da wata turjiya daga wajen 'yan
majalisar ba, kuma wannan bai ba da mamaki ba, idan aka yi laka'ari da irin
dasawar da bangaren zartarwa ke yi da na majalisar dokokin.

Shugaban majalisar dattawa, Senata Ahmed Lawan, ya tabbatar da wa shugaban
kasar cewa da majalisar dattawa da ta wakilai duka za su gaggauta zartar da
kasafin kudin, kamar yadda suka yi bara.

''Mun yi maka alkawari da 'yan Najeriya cewa mun shirya, kuma mun duƙufa
wajen nazari da zartar da kasafin kudin nan da karshen shekara.

''Muna la'akari da cewa yin hakan ya zama wajibi domin mun kawar da yanayin
nan na rashin tabbas da ke tattare da aiwatar da kasafin kudi, wanda ya yi illa
ga tattalin arzikinmu a shekarun da suka wuce, ta yadda za mu dore da shekarar
kasafin kudin aka fi so, mai farawa daga watan Janairu, ya kare a watan
Disamba.

Shugaban Najeriyar ya shaida wa 'yan majalisar dokokin cewa, jawabin da ya yi
taƙaitacce ne, don haka ma'aikatar kudi ce za ta yi cikakken bayani a kan duk
wani ƙabli da badin da kasafin kudin ya ƙunsa.

Tun da farko a ranar Laraba shugaban kwamitin kasafin kuɗi na Majalisar
Dattijan Najeriya Sanata Barau Jibril ya ce, gabatar da kasafin kuɗin na wannan
shekarar zai sha bamban da na sauran shekaru sakamakon annobar cutar
korona.

A cewarsa, za a bi ƙa'idojin kare yaɗuwar cutar da kuma yin tanadi ta yadda ba
za a samu cunkoso ba yayin gabatar da kasafin kuɗin, hakazalika ba za a daɗe
wurin gabatar da kasafin kudin ba kamar yadda ake yi ba a da.

An dai ɗora ƙudurin kasafin kuɗin na 2021 kan hasashen musayar dalar Amurka
ɗaya ga naira 379 da kuma mizanin gangar man fetur guda a kan dala 40, bisa
hasashen haƙo ganga miliyan 1.86 a kullum.

A bara dai an amince da kasafin kudin ne kan hasashen musayar dalar Amurka
ɗaya ga naira 305, haka kuma an saka mizanin gangar man fetur guda a kan
dala 57, bisa hasashen haƙo ganga miliyan 2.18 a kullum.

An sa ran shugaban yayin gabatar da kasafin kuɗin a ranar Alhamis, zai nanata
wasu kalaman ministar kuɗin ƙasar wadda ta bayyana cewa ƙudirin kasafin 2021
yana cike da burin bai wa ƙasar damar samun bunƙasa ta kowane ɓangare da
kuma zaburar da tattalin arziƙin Najeriya da samar da ayyuka.

Kalaman nata sun kuma haɗa da yauƙaƙa bunƙasar ƙasar, da samar da hanyoyin
zuba jari ga ababen more rayuwa, da inganta masana'antu da sana'o'in cikin
gida.

Sannan an sa ran wannan kasafin kuɗin na 2021 zai jaddada hasashen samun
jumullar kuɗin shiga naira tiriliyan 7.89 da kuma ƙunshin kasafin kamfanoni 60
mallakar gwamnati.

A bara dai, Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kan
kasafin kuɗin ƙasar na shekarar 2020, wanda ya kai naira tiriliyan
10,594,362,364,830.

Comments

Popular posts from this blog

JIRGIN RUWAN ANNABI NUHU DA AMURIKA TA KERA A SHEKARAR 2018

𝐍𝐈𝐆𝐄𝐑𝐈𝐀 @60:𝐌𝐔𝐋𝐊𝐈𝐍 𝐒𝐎𝐉𝐀 𝐌𝐀𝐒𝐔 𝐇𝐀𝐋𝐈𝐍 𝐓𝐒𝐈𝐘𝐀 𝐃𝐀 𝐍𝐀 𝐊𝐈𝐑𝐊𝐈

𝙔𝙖𝙣𝙙𝙖 𝙢𝙖𝙯𝙖𝙣𝙗𝙖𝙩𝙖 𝙠𝙚 𝙩𝙨𝙞𝙣𝙩𝙖𝙧 𝙠𝙬𝙖𝙧𝙤𝙧𝙤𝙣 𝙧𝙤𝙗𝙖 𝙨𝙪𝙣𝙖 𝙨𝙖𝙮𝙚𝙧𝙬𝙖 𝙟𝙖𝙢𝙖 𝙖