Posts

Showing posts from September 20, 2020

Halin da ƙasa take ciki- wasu jigajigai a APC sun bada hakuri.

Image
  Wasu jigajigan jam'iyyar APC mai mulki sun fara neman afuwar jama'ar Nigeriya. Wasu jiga-jigan 'yan jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya sun fara neman afuwar 'yan kasar a kan da su yi hakuri dangane da yanayin kunci da kasar take ciki yanzu haka sakamakon wasu matakai da gwamnatin kasar ke dauka da manufar gyara. Daya daga cikin jigo a jam'iyyar Farouk Adamu Aliyu, a cikin wata hira da ya yi da BBC, ya ce jama'a su yi hakuri da halin da ake ciki na matsi wanda ya ce dalilai ne suka haddasa hakan. Farouk Adamu Aliyu ya ce:"Ni ma a iya sanina ba na zaton an taba shiga kunci irin wannan na yanzu, kamar a bangaren abinci gaskiya ne an samu matsalar hauhawar farashi da dai sauransu". Ya ce abubuwa da dama ne suka kawo hakan, yana mai cewa mutane da dama sun sha kiransa ana yi masa Allah ya isa saboda yadda rayuwa ta yi kunci a yanzu. Jigo a jam'iyyar ta APC ya c:" Ga wadanda suke da-na- sanin tallafa mana da wani abu a lokacin da muke yakin ne...

Sarkin Zazzau ya rasu

Image
ASALIN HOTO Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa Allah Ya yi wa mai martaba Sarkin Zazzau Dokta Shehu Idris rasuwa. Ya rasu ranar Lahadi. Uban Garin Zazzau kuma Hakimin Soba, Alhaji Bashir Shehu Idris wanda ɗa ne ga marigayin shi ne ya tabbatar wa da BBC labarin. Rahotanni sun ce Sarkin ya rasu ne bayan gajeruwar jinya ta mako biyu a wani asibiti da ke Kaduna. Za mu ci gaba da kawo muku ƙarin bayani. Tarihin Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dokta Shehu Idris Haihuwa da Tsatson Sarki Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dokta Shehu Idris, an haife shi ne a watan Maris na shekarar 1936. Wanda ya haife shi ne Mai Unguwa Auta. Sunan na Auta aka fi sani, amma sunansa na Littafi shi ne Idrisu. Shi da ne, dan autan Mai Martaba Sarkin Zazzau Muhammadu Sambo. Shi kuma Sarki Muhamadu Sambo da ne, kuma na biyu a cikin 'ya'yan Sarkin Zazzau Malam AbdulKarim. Shi kuma Sarkin Zazzau Malam AbdulKarim shi ne na farko a daular Fulani karkashin jaddada addinin musulunci da Shehu Usumanu Danfodiyo y...