Sarkin Zazzau ya rasu
Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa Allah Ya yi wa mai martaba Sarkin Zazzau Dokta Shehu Idris rasuwa.
Ya rasu ranar Lahadi.
Uban Garin Zazzau kuma Hakimin Soba, Alhaji Bashir Shehu Idris wanda ษa ne ga marigayin shi ne ya tabbatar wa da BBC labarin.
Rahotanni sun ce Sarkin ya rasu ne bayan gajeruwar jinya ta mako biyu a wani asibiti da ke Kaduna.
Za mu ci gaba da kawo muku ฦarin bayani.
Tarihin Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dokta Shehu Idris
Haihuwa da Tsatson Sarki
Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dokta Shehu Idris, an haife shi ne a watan Maris na shekarar 1936. Wanda ya haife shi ne Mai Unguwa Auta. Sunan na Auta aka fi sani, amma sunansa na Littafi shi ne Idrisu. Shi da ne, dan autan Mai Martaba Sarkin Zazzau Muhammadu Sambo.
Shi kuma Sarki Muhamadu Sambo da ne, kuma na biyu a cikin 'ya'yan Sarkin Zazzau Malam AbdulKarim. Shi kuma Sarkin Zazzau Malam AbdulKarim shi ne na farko a daular Fulani karkashin jaddada addinin musulunci da Shehu Usumanu Danfodiyo ya yi a kasar Zazzau, kuma shi ne ya assasa gidan Katsinawa a sarautar Zazzau.
Ina Sarki ya taso?
Shi Mai martaba Sarki lokacin mahaifinsu yana Mai Unguwa a unguwar Iya a nan aka haife shi. Unguwar Iya wata unguwa ce da ke tsakanin unguwar Durumi da Kuyanbana. A nan ya girma, ya shekara akalla bakwai, inda har ya shiga makarantar allo, ya fara karatun addini.
A nan dai unguwar Iya ya yi makarantar farko da Bature ya gina a cikin birnin Zariya, wadda ake kira 'Town School one', ita ce kuma makaranatar 'Kofar Kuyanbana Local Government Education Primary School'. Yanzu ana ce mata 'Waziri rLawal Local Government Education Primary School', a nan ya fara karatu.
Bayan ya gama sai ya tafi Alhudahuda College, lokacin ana kiran makarantar da sunan 'Middle School'. Daga nan aka yi masa sauyi, ya koma makarantar koyar da malunta a Katsina lokacin ana kiran ta 'Katsina Teachers' College'.To, a nan ya koyi aikin koyarwa, wanda shi ne babbar sana'arsa ta farko da ya iya.
Daga baya mai martaba ya sauya daga malamin makaranta ya shiga aikin mulki, wanda har ya je kasar Ostireliya (Australia). Yana cikin daliban farko da ofishin jakadancin Ostireliya suka dauki dawainiyarsu suka je suka yi karatu na koyon ilimin mulki a kasar ta Osireliya
Wuraren da ya yi aiki
Daga shekarar 1956 ya koyar a wurare daban-daban a cikin garin Zariya da kauyuka. Ya koyar a Zangon Aya, ya koyar a Paki, har ya yi hedimasta a Pakin. Ya kuma yi hedimasta a Hancin Kare a makarantar 'Town School No.3''.
A shekarar 1962 ya koma aikin mulki, lokacin da ya koma karkashin hukumar 'NA' (Native Authority) ta Zariya a zamanin Sarkin Zazzau Aminu. Inda ya gwama aiki biyu, wato yana aiki a hukumar 'NA', kuma yana aiki a matsayin jami'in sadarwa na hukumar kula da kananan hukumomi da masarautu na jihar Arewa.
Daga baya Mai Martaba Sarkin Zazzau Muhammadu Aminu ya ba shi mukamin Babban sarakatare na musamman na sarki. Daga nan ne sai aka nada shi sarauta, ya zama wakilin ofis, wato mai daukar nauyin duk abin da ya shafi aikin masarauta a karkashin 'Native Authority' a wannan lokacin.
Ya rike wannan mukami na tsawon kamar shekara biyu zuwa uku, sai Mai Martaba Sarkin Zazzau Muhammadu Aminu ya nada shi hakimin birni da kewaye, mukamin da ya rike na tsawon shekara biyu zuwa uku, yana hakimi. Kuma Dan Madamin Zazzau.
A shekarar 1975 likafarsa ta yi gaba, aka ba shi a sarautar Sarkin Zazzau.
Sauyin da ya kawo a sarautar Zazzau cikin shekaru arba'in da biyar yana mulki
Comments
Post a Comment