Halin da ƙasa take ciki- wasu jigajigai a APC sun bada hakuri.
Wasu jigajigan jam'iyyar APC mai mulki sun fara neman afuwar jama'ar Nigeriya.
Wasu jiga-jigan 'yan jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya sun fara neman afuwar 'yan kasar a kan da su yi hakuri dangane da yanayin kunci da kasar take ciki yanzu haka sakamakon wasu matakai da gwamnatin kasar ke dauka da manufar gyara.
Daya daga cikin jigo a jam'iyyar Farouk Adamu Aliyu, a cikin wata hira da ya yi da BBC, ya ce jama'a su yi hakuri da halin da ake ciki na matsi wanda ya ce dalilai ne suka haddasa hakan.
Farouk Adamu Aliyu ya ce:"Ni ma a iya sanina ba na zaton an taba shiga kunci irin wannan na yanzu, kamar a bangaren abinci gaskiya ne an samu matsalar hauhawar farashi da dai sauransu".
Ya ce abubuwa da dama ne suka kawo hakan, yana mai cewa mutane da dama sun sha kiransa ana yi masa Allah ya isa saboda yadda rayuwa ta yi kunci a yanzu.
Jigo a jam'iyyar ta APC ya c:" Ga wadanda suke da-na- sanin tallafa mana da wani abu a lokacin da muke yakin neman zaben Shugaba Buhari musamman a shekarar 2015, to muna neman su yi mana gafara".
Farouk Adamu Aliyu ya ce ba yana bayar da wannan hakuri ne domin wani abu ko kuma yana nadama a kan ja gaban da suka yi wajen ganin Shugaba Buhari ya samu nasara a zaben, sam ko kadan baya nadama in ji shi
Ya ce ya bayar da wannan hakuri ne domin ba yadda za ka yi ka daki mutum sannan ka hana shi kuka.
"Ina so na ja hankalin talakawan Najeriya a kan su yi la'akari da cewa mu masu hannu da shuni da dan APC da dan PDP, uwarmu daya ubanmu daya".
"Bambanci da ke tsakanin jamiyyun nan bai wuce jagoranci ba. Misali na amince da Shugaba Buhari ba ya almundahana. Kuma ba za a hada kai da shi ba a yi. Wallahi tallahi ni Farouk Adamu duk lokacin da na gamsu cewa shugaba Buhari yana almundahana to zan bar shi," a cewarsa.
Ya ce ya kamata talakawa su gane idan har an zo zabe za ka iya yin jam'iyyarka, amma idan har kana gani jam'iyyarka ba ta tsayar da wanda ya dace ba to ka zabi wanda kake gani zai biya bukatunka.
Dangane kuma da rikicin jam'iyyar tasu ta APC, Farouk Adamu ya ce "lallai jamiyyar na tattare da rikice-rikicen cikin gida kamar yadda yake a kowace babbar jamiyya a duniya.
Saboda haka muna yin dukkan maiyiwuwa wajen yin sulhu ga 'yayan jam'iyya domin tunkarar zaben 2013".
Comments
Post a Comment