Posts

Showing posts from February 7, 2020

Gwamna Zulum ya nuna rashin sha'awarsa na wani ya yi masa tattakin karramawa.

Image
'Ka sha zamanka ka huta na gode da kauna'- Sakon Gwamna Zulum ga matashi da ya fara tattaki daga Jigawa zuwa Maiduguri. Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi kira ga matashi Usman Zubairu, wanda ya sanar da cewa zai yi tattaki daga jahar Jigawa zuwa Maiduguri domin jinjinawa gwamnan kan ayyukan da yake yi cewa yayi zamansa amma ya gode. Gwamnan ya bayyana hakan ne da yammacin Juma'a a shafinsa na Tuwita Yace: "A'a, Nagode, dan uwa Usman Zubairu." Ya kara da cewa; "Na samu wani labarin cewa wani matashin dan uwa Usman Zubairu, ya kaddamar da tattaki daga Jigawa zuwa Maiduguri domin karramani." Ya ci gaba da cewa "Ina mai matukar godiya Malam Usman bisa ga goyon bayarka amma ina rokonka ya ajiye wannan tafiya." "A nawa fahimtar, ya zo Maiduguri tuni. Ina kira garemu mu sanya jihar Borno da Najeriya cikin addu'o'inmu. Hakan ya fi kyau." Usman Zubairu dai ya bayyana cewa zai yi tattaki daga jihar...

Batanci Ga Alzakzaky Ya Ja Wa Wani Matashi Hukunci A Kotu.

Image
Wata Kotu ta daure wani Matashin akan ya yi 6atanci da Hoton Shaikh Alzakzaky. A ranar talatar na da ta gabata (4/2/2020) ne, wata Kotun Majistare da ke Potiskum jihar Yobe ta yanke wa wani matashi mai suna Mohamad Garba hukuncin daurin watanni shida a gidan kaso ko kuma tarar Naira dubu 10,000 a bisa samunsa da laifin 6ata sunan Malamin Addinin Musulunci shugaban 'yan uwa Musulmi a Najeriya, Shaikh Alzakzaky,ta hanyar amfani da Hoton Malamin a cikin wani bidiyon 6atanci da ya yi wa wasu Mata ya sakie shi a kafafen sadarwa. Bidiyon mai tsawon mintuna biyu da dakika 40 da Matashin ya saki kafafen sadarwa na zamani a ranar 26 ga Janairun 2020,ya nuna yadda yake 6atanci ga wasu matan da ba su da Hijabi a jikinsu yana kuma tallatasu da cewa "ana gwanjonsu",a inda daga karshen bidiyon ya dauka da Hoton Malam Alzakzaky, sakamakn haka Almajiran Malamin suka yi kararsa da sunan ya yi 6atanci da zub da Mutunci wa Malamin nasu. Almajiran Malamin sun binciko matashin sukakuma ...

Kotu Ta Ba Da Umurnin A Rika Barin Likitocin Alzakzaky Suna Ganawa Da A Duk Sadda Ya Bukaci Hakan.

Image
SHARI'AR SHEIKH ALZAKZAKY: Kotun Tarayya da ke Kaduna a zamanta na yau Alhamis domin ci gaba da sauraren Karar da gwamnatin Jahar ta shigar akan wasu tuhumce-tuhumce da ta ke yi wa Jagoran 'yan uwa Musulmi Shaikh Ibraheem Alzakzaky da mai dakinsa Malama Zeenatu,Kotun ta ba da umurnin a rika barin Likitocin Shehin Malamin su rika duba lafiyar sa a cikin gidan Yari a duk lokacin da suka bukaci haka. Shehin Malamin dai na ci gaba da tsarewa ne tun Watan Disambar 2015,biyo bayan kashe daruruwan Almajiransa, 'yayansa da wasu 'yan uwansa na jini a yayin da shi kansa da Matarsa ba su tsira daga halbin harsasan da Sojoji suka yi masu wanda har yau suke cikin rashin lafiya sakamakon illar da harsasan su kai masu a jiki. Za dai a ci gaba da sauraren karar ne a ranar 24 da 25 na watan da muke ciki,bayan rashin halartar Malamin da Matarsa a zaman Kotun na yau sakamakon rashin lafiyar da ke su fama da ita, kamar yadda Lauyan Malamin Femi Falana ya bayyana. Menene ra'ayinku...