Gwamna Zulum ya nuna rashin sha'awarsa na wani ya yi masa tattakin karramawa.
'Ka sha zamanka ka huta na gode da kauna'- Sakon Gwamna Zulum ga matashi da ya fara tattaki daga Jigawa zuwa Maiduguri.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi kira ga matashi Usman Zubairu, wanda ya sanar da cewa zai yi tattaki daga jahar Jigawa zuwa Maiduguri domin jinjinawa gwamnan kan ayyukan da yake yi cewa yayi zamansa amma ya gode.
Gwamnan ya bayyana hakan ne da yammacin Juma'a a shafinsa na Tuwita Yace: "A'a, Nagode, dan uwa Usman Zubairu."
Ya kara da cewa; "Na samu wani labarin cewa wani matashin dan uwa Usman Zubairu, ya kaddamar da tattaki daga Jigawa zuwa Maiduguri domin karramani."
Ya ci gaba da cewa "Ina mai matukar godiya Malam Usman bisa ga goyon bayarka amma ina rokonka ya ajiye wannan tafiya."
"A nawa fahimtar, ya zo Maiduguri tuni. Ina kira garemu mu sanya jihar Borno da Najeriya cikin addu'o'inmu. Hakan ya fi kyau."
Usman Zubairu dai ya bayyana cewa zai yi tattaki daga jiharsa ta Jigawa zuwa Maiduguri domin nuna goyon baya ga gwamna Zulum kan namijin kokarin da yake
yi ga al'ummarsa.

Comments
Post a Comment