๐ซ๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐ฎ๐๐๐๐๐๐ ๐ฉ๐๐๐๐ ๐ฏ๐๐๐.
Babagana Umara Zulum: 'Da jaki mayaฦan IS suka kai wa Gwamnan Borno hari'
Gwamnatin jihar Borno da ke Najeriya ta ce mayaฦan da ke da alaฦa da ฦungiyar IS reshen Afrika Ta Yamma wato ISWAp, sun yi amfani da jaki wajen kai wa gwamnan jihar Babagana Umara Zulum hari.
A ranar Lahadi Gwamna Zulum ya tsira da ga harin da mayakan na IS suka yi ikirarin kai masa, ko da yake ca a samu asarar rai ba.
Harin dai ya faru ne kusan sa'a 48 bayan da masu ta da ฦayar baya suka afka wa tawagar gwamnan a yankin Baga inda kimanin mutum 30 suka mutu a harin - har da sojoji da ฦดan sanda.
Kwamishinan Shari'a na jihar Borno, Barista Kaka Shehu Lawan, wanda yake cikin tawagar gwamnan da ta tsallake rijiya da baya a hare-hare biyu, ya shaida wa BBC cewa harin farko ya faru ne bayan sun tashi daga Monguno zuwa Baga.
"Muna hanya daga Monguno zuwa Baga sai 'yan ta'adda suka sa bama-bamai da ake tashi ta hanyar amfani da ''remote control'' a wurare uku daban-daban. Dukkan bama-baman sun tashi a lokaci guda.
''Daga nan suka bi mu da harbi. An kwashe minti fiye da 20 ana harbe-harbe kafin 'yan ta'addan su janye," a cewarsa.
Barista Lawan ya ce mayakan Boko Haram sun yi musu kwanton-ษauna ne yana mai cewa ana tsaka da harbe-harbe sai jami'an tsaro suka umarci motar da gwamnan ke ciki ka da ta yi gaba.
A cewarsa, a lokacin da suke kan hanyar koma wa gida mayakan Boko Haram sun ษaura wa "jaki bam aka sa masa jarkoki irin na ruwa kamar wanda zai je diban ruwa.
"Su wadannan miyagun mutanen suna ษoye a baya, to shi ne shi sojan da yake kan mota ya ษauke jakin da bindiga. Sai bam ya tashi, sannan waษannan miyagun mutane suka riฦa harbi da bindiga."
Ya kara da cewa gwamnan da jami'an gwamnati, cikinsu har da kwamishino hudu ne a cikin tawagar amma babu abin da ya same su.
Comments
Post a Comment