๐’๐ก๐ฎ๐ ๐š๐›๐š ๐๐ฎ๐ก๐š๐ซ๐ข ๐ง๐š ๐๐ข๐ฃ๐ž๐ซ๐ข๐š ๐ฒ๐š ๐Ÿ๐š๐๐ข ๐๐š๐ฅ๐ข๐ฅ๐ข๐ง ๐ค๐ข๐ง ๐œ๐ข๐ซ๐ž๐ฐ๐š ๐Œ๐š๐ฅ๐ข ๐ญ๐š๐ค๐ฎ๐ง๐ค๐ฎ๐ฆ๐ข

 Buhari ya faษ—i dalilin ฦ™in cire wa Mali takunkumi

Mali

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce akwai wasu "batutuwa da ake bukatar warwarewa" a game da shirin sojin Mali na mika mulki ga farar hula kafin kungiyar Ecowas ta cire takunkumin da ta sanya wa kasar.

Ecowas ta sanya wa Mali takunkumin ne bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa Shugaba Ibrahim Boubacar Keรฏta a watan jiya.

Daya daga cikin sharudan janye wa kasar takunkumi shi ne nada shugaba da firaiminista farar hula.

Kodayake sojojin sun cika wannan sharadi, shugabansu Kanar Assimi Goita yana ci gaba da zama a matsayin mataimakin shugaban kasa, lamari da har yanzu bai gamsar da Ecowas ba.

Ofishin Shugaba Buhari ya fitar da sanarwar cewa watakila shugabannin kasashen Yammacin Afirka za su sake ganawa domin tattaunawa kan rikicin siyasar Mali, bayan ya gana da wakilin Ecowas kuma tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.

"A cewar wakili na musamman, har yanzu shugabannin sojin ba su cika sharudan Ecowas ba na nada farar hula a matsayin mataimakin shugaban kasa, da kuma irin rawar da zai taka a gwamnati," a cewar sanarwar.

Comments

Popular posts from this blog

JIRGIN RUWAN ANNABI NUHU DA AMURIKA TA KERA A SHEKARAR 2018

๐๐ˆ๐†๐„๐‘๐ˆ๐€ @60:๐Œ๐”๐‹๐Š๐ˆ๐ ๐’๐Ž๐‰๐€ ๐Œ๐€๐’๐” ๐‡๐€๐‹๐ˆ๐ ๐“๐’๐ˆ๐˜๐€ ๐ƒ๐€ ๐๐€ ๐Š๐ˆ๐‘๐Š๐ˆ

๐™”๐™–๐™ฃ๐™™๐™– ๐™ข๐™–๐™ฏ๐™–๐™ฃ๐™—๐™–๐™ฉ๐™– ๐™ ๐™š ๐™ฉ๐™จ๐™ž๐™ฃ๐™ฉ๐™–๐™ง ๐™ ๐™ฌ๐™–๐™ง๐™ค๐™ง๐™ค๐™ฃ ๐™ง๐™ค๐™—๐™– ๐™จ๐™ช๐™ฃ๐™– ๐™จ๐™–๐™ฎ๐™š๐™ง๐™ฌ๐™– ๐™Ÿ๐™–๐™ข๐™– ๐™–