๐๐ก๐ฎ๐ ๐๐๐ ๐๐ฎ๐ก๐๐ซ๐ข ๐ง๐ ๐๐ข๐ฃ๐๐ซ๐ข๐ ๐ฒ๐ ๐๐๐๐ข ๐๐๐ฅ๐ข๐ฅ๐ข๐ง ๐ค๐ข๐ง ๐๐ข๐ซ๐๐ฐ๐ ๐๐๐ฅ๐ข ๐ญ๐๐ค๐ฎ๐ง๐ค๐ฎ๐ฆ๐ข
Buhari ya faษi dalilin ฦin cire wa Mali takunkumi Reuters Copyright: Reuters Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce akwai wasu "batutuwa da ake bukatar warwarewa" a game da shirin sojin Mali na mika mulki ga farar hula kafin kungiyar Ecowas ta cire takunkumin da ta sanya wa kasar. Ecowas ta sanya wa Mali takunkumin ne bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa Shugaba Ibrahim Boubacar Keรฏta a watan jiya. Daya daga cikin sharudan janye wa kasar takunkumi shi ne nada shugaba da firaiminista farar hula. Kodayake sojojin sun cika wannan sharadi, shugabansu Kanar Assimi Goita yana ci gaba da zama a matsayin mataimakin shugaban kasa, lamari da har yanzu bai gamsar da Ecowas ba. Ofishin Shugaba Buhari ya fitar da sanarwar cewa watakila shugabannin kasashen Yammacin Afirka za su sake ganawa domin tattaunawa kan rikicin siyasar Mali, bayan ya gana da wakilin Ecowas kuma tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan. "A cewar wakili na musamman, har yanzu shugabannin sojin ba su c...