Amurika na neman diyyar Dala biliyan daya da rabi wajen Iran.


Wata sabuwa inji yan caca'
Amurka na neman diyar Dala biliyan daya da rabi daga wajen Iran.




Wata kotu a Amurka ta yanke wani hukunci mai kama da almara cewar Iran zata biya iyalan tsohon dan leken asirin FBI Mr.Robert Livinson dalar Amurka kimanin $1.4bl sakamakon batar dabon da dan kwangilar yayi yayin wata ziyarar da ya kai zuwa wani tsibiri a cikin Iran din a shekarar 3/2007.
Da farko Amurka ta shigar da karar Iran ga MDD,daga baya kuma kasar Swiss ta shiga tsakani domin samo bakin zaren sasantawa ta fuskacin diflomasiyya.
-
Ana hakan ne katsam,a farkon wannan shekarar ta 2020 sai iyalan Mr.Livinson suka bayyana cewar basu da ragowar sauran fata game da mahaifin nasu,sun tabbatar da cewar,bayanan sirrin da suka samu ya tabbatar musu da rasuwar uban nasu a hannun Iran. Don haka suna neman gwamnatin Amurka da ta nema musu hakkin su daga wuyan Iran.
-
Sai kuma ga wata kotun Gunduma (District Court) ta yanke hukuncin cewar,bisa wasu kwararan dalilan da ta samu daga iyalan Mr.Livinson da kuma wasu bangarorin na daban,lallai ta gamsu cewar,Mr.Livinson ya mutu ne a kurkukun Iran bayan an daure shi tsawon shekaru 13 tare da gana masa ukuba.
Don haka ya umurci gwamnatin Iran da ta biya Iyalan Mr.Livinson Kudi Dalar Amurka har biliyan daya da rabi.
-
Alkalin Kotun Mr.Timothy Kelly ya bayyana cewar yayi amfani ne da shedar kwararru tare da tabbatattun bayanai daga iyalan Mr.Livinson din inda ya yanke hukuncin cewar,dole Iran ta baiwa iyalan Mr.Livinson dala $107m sannan kuma bisa horarswa tare da ladabtarwa ga Iran, Iran din zata biya tsabar kudi dala $1.3bl ga Amurka. Alkalin ya bayyana cewar,da gangan jami'an leken Asirin Iran suka yaudari jami'in FBI din Mr.Livinson kana suka sace shi,bayan ya mutu a kurkukunsu sai suka batar da gawar suka ce wai da kansa ya fice daga kasar ta Iran,kuma wai basu san inda ya tafi ba tunda ya fice daga Iran din.
Alkalin yace wannan ai rainin hankali ne da kuma wofantar da mutane. Don haka Iran ta cancanci wannan hukuncin mai tsaure.
-
Iayalan Mr.Livinson sun bayyana gamsuwarsu ga wannan hukuncin da Alkalin ya yanke wa Iran,kuma sun bayyana cewar zasu karbi wannan kudin bisa hakuri,amma ba domin ya kai kimar Uban nasu bane inji Matar Livinson.
Sun bayyana cewar,sun kwashe shekara 13 cikin damuwa da fargaban rashin sanin halin da uban nasu yake ciki,amma yanzu kam sun dan fara samun nutsuwa.
-
A janibin Iran kuwa,har yanzu bata fitar da wani bayani a kan wannan hukuncin ba,amma masana a ciki da wajen Iran din sun bayyana cewar wannan tamkar fashi da shari'a ne Amurkan ke son yi wa Iran din sakamakon wani hukuncin da kotun MDD ta yanke na cewar Amurka ta mika wa Iran din biliyoyin dalolin Iran dake hannunta,wanda Amurkan ta kwace tun bayan nasarar juyin juya halin musulnci a 1979.
 Don haka ne ake ganin cewar wata dubara ce ta Amurka domin ta cinye kudin Iran din dake hannunta.
Amma in ba haka ba me yasa Alkalin bai nemi Iran din ba domin ta kare kanta a gabansa ba?
-
Masana harkar tsaro da diflomasiyya da dama sun nuna cewar,wannan wata kulalliya ce wacce kungiyar leken asirin Amurka ta CIA  da FBI din suka shirya tare da hadin bakin wannan Alkalin domin sace wa Iran din dukiyarta wacce tun farko wata kotu tayi hukuncin cewar ta mika wa Iran din hakkinta.
----
NIA
7/10/2020
.

Comments

Popular posts from this blog

JIRGIN RUWAN ANNABI NUHU DA AMURIKA TA KERA A SHEKARAR 2018

๐๐ˆ๐†๐„๐‘๐ˆ๐€ @60:๐Œ๐”๐‹๐Š๐ˆ๐ ๐’๐Ž๐‰๐€ ๐Œ๐€๐’๐” ๐‡๐€๐‹๐ˆ๐ ๐“๐’๐ˆ๐˜๐€ ๐ƒ๐€ ๐๐€ ๐Š๐ˆ๐‘๐Š๐ˆ

๐™”๐™–๐™ฃ๐™™๐™– ๐™ข๐™–๐™ฏ๐™–๐™ฃ๐™—๐™–๐™ฉ๐™– ๐™ ๐™š ๐™ฉ๐™จ๐™ž๐™ฃ๐™ฉ๐™–๐™ง ๐™ ๐™ฌ๐™–๐™ง๐™ค๐™ง๐™ค๐™ฃ ๐™ง๐™ค๐™—๐™– ๐™จ๐™ช๐™ฃ๐™– ๐™จ๐™–๐™ฎ๐™š๐™ง๐™ฌ๐™– ๐™Ÿ๐™–๐™ข๐™– ๐™–