'YAN SHI'A A NAJERIYA SUN GUDANAR DA TATTAKI

'Yan shi'a sungudanar da Tattaki a Najeriya.



Yan shi'a daga yankin panbeguwa
Kamar ko wace shekara 'yan shi'a mabiya El'zakzaky a Najery suna gudanar da Tattaki domin kwatanta irin abinda ya faru ga jikan Annabi (S) sayyadi Husain.

'Yan shi'ar sunbi sahun takwarorin su na sassan duniya da suke takawa a kasa zuwa birnin karbala domin ziyarar sayyadina Husain. 

A Najeriya 'yan shi'ar suna tashi ne daga bangarori shida zuwa Zariya su karkare tattakin nasu a can kuma suyi addu'a da jawabi daga bakin Sheikh El'zakzaky.

Amma tun bayan arangama da aka samu tsakanin su, da sojoji a shekarar 2015 wanda yayi sanadiyyar mabiya malamin 347 a rahoton gwamnatin, da jikkata wasu da dama, gami da kama Sheik El'zakzaky da matarsa, yasa suka janye da zuwa cikin Birnin na Zariya domin kaucewa wata matsalar.

Duk da haka a wasu lokutta ana samun kashe kashe daga jami'an tsaro abisa hanyar tasu kafin zuwa inda zasu karkare tattakin kamar a kano da aka taba samun asarar rayuka da dama, shekarar 2016 dakuma kaduna da sauran daidaiku.

Wasu na ganin cewa miyasanya 'yan shi'an mabiya El'zakzaky bazasu iya hakura da wan'nan tattakin ba duba da yanda ake samun asarar rayuka maza da mata wani lokacin ma harda kana'nan yara?

Wakilin mu ya Zanta da wani daga cikin 'yan shi'ar kan wan'nan batu yace"Mu addini muke kuma dokar kasar tabawa kowa dama yayi addini iya fahimtar sa kuma har  ama bashi tsaro, Amma mu kashemu akeyi"

#HRtv to bazaku iya hakuri ba duba da yanda ake samun asarar rayuka lokaci zuwa lokaci?

YACE:"Yakamata ne ka tambayi masu kashe mu bazasu iya hakuri su daina kashe mu ba? Suma ai masu hankali ne kuma suna da 'ya'ya suna da iyaye sun san zafin rasa rai amma miyasa bazasu iya kyalemu muyi addinin mu yanda muka fahimta ba? Yau ba mun fita ba, kuma munyi muntashi lafiya? 

Inda basu so atashi lafiya ba ai da sun kawo mana hari, kaga ashe sune ka takular ba mu ke takula ba.

#HRtv: Amma ance kuna tare hanya kuna takura ma mutane.

YACE: Ai yanzu gabanka ake kaga gayanan mutane na wucewa ga motoci ina muka tare hanya? Kuma idan mun tare hanya shine hukuncin kisa?

#HRtv: Wane kira zakayi ga gwamnati dama sauran Al'uma?

YACE: kirana dai guda daya ne kuma ita gwamnatin ta sanshi kuma kullum tana jin shi, ba ma ni kadai ba duk wani mai imani da ruhi irin na 'yan adam taka yayi mata irin wan'nan kiran"Shine tasako mana Malamin mu da matar sa yaje ya nemi lafiya, yana fama da ciwo da guba ajikin sa tsawon shekara biyar kuma kotu ta sake shi,amma ita gwamnatin da yake tana da manufa taki sakin sa, Sauran mutane kuma yakama su fahimce mu, mudai addini muke kuma iyakar fahimtar mu kenan, kuma su sani shi hannun azzalumi tsawo gareshi alokacin da aka zalumci wani kaji dadi, wataran kanka azzalumin zaiyo.


Comments

Popular posts from this blog

ππˆπ†π„π‘πˆπ€ @60:πŒπ”π‹πŠπˆπ π’πŽπ‰π€ πŒπ€π’π” π‡π€π‹πˆπ π“π’πˆπ˜π€ 𝐃𝐀 𝐍𝐀 πŠπˆπ‘πŠπˆ

YANDA AKE RUBUTA LABARI

JIRGIN RUWAN ANNABI NUHU DA AMURIKA TA KERA A SHEKARAR 2018