DANGANTAKAR DAUKAR NAUYIN FILMS DA ISAR DA SAKO

Dangantakar Daukar Nauyin Shirya Fim Da Isar Sa'ko?

A wannan zamani fim ya Zama tamkar Hantsi leka Gidan Kowa, da wuya ka sami wani mutum daya wanda bashi da alaka da fim ko da kuwa ta kallo ce. Wani sanannen abu kuma shi ne kadan ne daga cikin mutane masu kallon Fim suke da masaniya akan dalilin da yasa ake shirya fim har ya zo gare su su kalla.

A fiye da shekaru 100 da suka gabata zuwa yau Fim ya shiga jerin Hanyoyin isar da sako mafi sauri da kuma saukin fahimta. Wannan dalilin yasa 'yan mulki mallaka suka rungumi wannan hanya ta fim wajen yada manufofinsu ga sauran Al'umma.

Wasu al'ummun ba su yi fargar jaji ba sun lura da wuri irin barnar da Fim din Turawa ya soma haifarwa a cikin Al'ummar su musamman ga matasa, ganin haka sai suma suka soma shirya fim domin kare kai. Duk Wanda ya Kalli Fima-Fimai na Indiya a Farkon al'amarin Fim din su zaka ga ba komai a ciki sai yada al'adunsu,  sun yi hakan ne kuwa domin mayar da martani ga harin da 'yan mulkin Mallaka suka kawo musu da Fim har cikin gida, kuma a gaskiya sun ga tasirin matakin da suka dauka, ba Indiya kadai ba wurare da dama sun dau irin wannan matakin hatta a tsakaninsu Turawan sun rinka kaiwa juna farmaki da Fima-Fimai saboda bambancin Akida da kuma al'ada.

To Amma mu a nan Afirka a daidai wannan lokaci sai muka zama jujin zube tarkacen Fima-Fimai Turawa, suma sauran musamman Indiya da Chanis da suka lura banza ta fadi sai suka shiga angizo nasu, kafin kiftawa da Bisimillah mutanenmu masu kallon Fim wasu sun rungumi al'adun Turawa musamman Amurkawa Kaboyi, wasu kuma Indiyawa wasu Chanis saboda tasirin da Fima-Fimai suka yi musu.

Wata barna kuma da 'yan Mulkin Mallaka suka yiwa Afirka game da fim shi ne; su da kansu ne suke shirya Fim akan mutanen Afirka, inda suka rinka nunawa duniya cewar mutanen Afirka fa musamman Bakaken fata wasu dazawa ne ba su da maraba da dabbobi.

Fima-Fimai irinsu; Tarzan, King Solomon's Mines, African Queen, God must be crazy----- Duk su suka shigo Afirka suka shirya su ba don komai ba sai don su nuna Afirka da Bakaken fata a matsayin banzaye, dolaye, jahilai, Abokan dabbobi.

Faransa har wata doka ta kafa a kasashen Afirka da take yiwa Mulkin Mallaka kan cewa babu wani 'Dan kasa da ya ke da ikon shirya Fim, sai su Faransawa. Wato bama jikkunanmu da dukiyarmu kadai suka mallaka ba harda fasaharmu da tunaninmu, sun yi hakan ne kuwa domin suna da masaniya akan irin tasirin Fim wajen sauya tunanin Al'umma.

Kafin kasashen Afirka su soma samun 'yancin kai, Fim kadan ne aka shirya su akan barnar Turawa a Afirka, suma kadan din ba a kyale su ba. Misali da Chris Maker da Alain Resnais suka shirya wani Fim da Faransanci akan yadda Turawa suka sace kayayyakin al'adun Afirka Mai suna 'LESS STATUE MEURENT AUSSI' da kuma wani da Rene Vautier ya shirya mai suna 'AFRIQUE 50', gaba dayansu dakatar da nuna su aka yi na tsawon shekara 10 ba domin komai ba sai don kar a tona asirin barnarsu.

Da haka zamu iya lura lallai Fim yana da karfi da kuma tasiri kuma makami ne ga duk wanda yake so ya yaki ko yada wata manufa tasa ga wata al'umma yake rika da karfi.

To ko da aka shigo karni na 21, manufar shirya Flfim ba ta sauya ba, sai gwamnatoci, kungiyoyi, addini, kungiyoyi masu zaman kansu, kamfanoni da cibiyoyin tattalin Arziki, 'yan siyasa, rundunonin mayaka, kungiyoyin Asirai, masu kimiyyar zamani, duk suka rungumi Fim a matsayin daya daga cikin manyan hanyoyinsu na yada farfagandar manufofinsu. Domin cimma sai suka janyo manyan masana harkar fim a jika suna shirya musu fim su kuma suna daukar nauyinsa.

Idan kun nazarci rubutu na tunda fari zaku ga shi Fim tun asalinsa samun nasararsa ya dogara da fuka-fukai guda biyu ne, na farko; masu shirya Fim wadda ta kanshi ma'aikata da kuma Aktoci.
Na biyu kuma; masu daukar nauyin shirya Fim su ba su da iyaka. Ya danganta Wlwanne sako ake so a isar, wani lokaci su masu daukar nauyin ne suke neman masu shirya Fim da su shirya musu Fim akan kaza za su dau nauyinsa. Wani zubin kuma su masu shirya Fim ne ke neman masu Daukar Nauyin wani Fim da suka tsara sai su duba su gani idan ya dace da manufofinsu sai a sasanta, kuma wannan ne ya fi faruwa, kai harma ya zama al'adar Fim Farautar wadanda za su dauki nauyin wani Fim da Aka tsara, wato a Duniyar masana'antar Fim ba abin kunya bane ka dau tallar Fim dinka da ka tsara a rubuce kana neman wadanda za su dau nauyin shirya shi. Bil hasali ma a jarumta ne, ana kallon wanda ya kware a iya nemo masu daukar nauyin Fim a matsayin jarumi ne.

A duniyar da suka dauki Fim da muhimmanci a yanzu manyan kamfanoni ake da su wanda aikinsu shi ne tallar Fim din da ba a riga an yi ba. Ku natsu da kyau zan baku labarin wani abin mamaki akan wani shahararren mai tallan fim.

Ina fatan zaku yi mini hakuri sai mun hadu a ci gaban wannan Rubutun.

©Muhammad Rajab Muhammad
08037756736
04/11/2019

Comments

Popular posts from this blog

JIRGIN RUWAN ANNABI NUHU DA AMURIKA TA KERA A SHEKARAR 2018

๐๐ˆ๐†๐„๐‘๐ˆ๐€ @60:๐Œ๐”๐‹๐Š๐ˆ๐ ๐’๐Ž๐‰๐€ ๐Œ๐€๐’๐” ๐‡๐€๐‹๐ˆ๐ ๐“๐’๐ˆ๐˜๐€ ๐ƒ๐€ ๐๐€ ๐Š๐ˆ๐‘๐Š๐ˆ

๐™”๐™–๐™ฃ๐™™๐™– ๐™ข๐™–๐™ฏ๐™–๐™ฃ๐™—๐™–๐™ฉ๐™– ๐™ ๐™š ๐™ฉ๐™จ๐™ž๐™ฃ๐™ฉ๐™–๐™ง ๐™ ๐™ฌ๐™–๐™ง๐™ค๐™ง๐™ค๐™ฃ ๐™ง๐™ค๐™—๐™– ๐™จ๐™ช๐™ฃ๐™– ๐™จ๐™–๐™ฎ๐™š๐™ง๐™ฌ๐™– ๐™Ÿ๐™–๐™ข๐™– ๐™–