RAHOTANNI DAGA BAGHADAD TA KASAR IRAQ

Rahotanni sun bayyana cewa;Jakadan Amurka ya tsere daga Bagagaza sakamakon boren Al'umma.

Daga Awwal Isa Musa

Bayan ayyana zaman makoki na kwana 3 wanda Firaministan riko na Iraqi Adel Abdul Mahdi yayi,da kuma furucin Allah wadai ga Amurka wanda babbabn marja'in Addini na Iraqi yayi ga Amurka,dubban mutane sun fito zanga-zangar la'anta da kin jinin Amurka a biranen Iraqi da dama.

Mutanen da suka yi kwamba suka mamaye ofishin Jakadancin Amurka dake birnin Bagadaza,suna kiran "mutuwa ga Amurka!mutuwa ga Israila!sannan suna kiran da a kamo jakadan a hukunta shi.

 Hakan ya tilasta tserewar Jakadar daga ofishinsa dake " Green Zone" zuwa wata mabuya ta daban,abin da har yanzu an ki a bayyana inda jakadan ya buya. An bayyana cewar,an ga wasu da boyayyun fusaku cikin bakaken mota suna tserewa,daga nan aka sanar da ficewar jakadan.

Masu zanga-zangar na kira da "Tilas a rufe ofishin jakadancin Amurka dake Baghdad, Iraqi,kuma tilas majilisar kasar tayi dokar korar sojojin Amurka daga kasar ta Iraqi.

An bayyana cewa,wasu 'yan tsiraru ne kawai suka rage a cikin Ofishin na Amurka dake Baghadad. Wasu ma sun fara kafa Tamfal domin yin zaman dirshan har sai an rufe ofishin jakadancin na Amurka a Baghdad.

Da farko an yi yunkurin dakile masu boren,amma lamarin ya gagari Kundila,sakamakon bulbulowar al'umma.

Shugaban kungiyar gwagwarmaya ta "Asa'ib Ahlal Haq Shaikh Qais al-Khazli ya bayyana wa masu zanga zangar cewar, "ba ma kaunar Amurka a kasarmu,ba ma son komai nasu,domin sune tushen duk wata fitina a kasar Iraqi."

 Haka zalika Rundunar IRGC ta Iran tayi kira ga Iraqawan da su dauki fansa kan Amurka,domin dokokin kasa da kasa sun halasta musu yin hakan.Haka zalika ita ma Kungiyar Hizbullahi ta Lebanon tayi Allah wadarai da harin,ta bayyana shi da dabbancin kauyawa.Sannan tayi kira ga kungiyar Hizbullahi ta Iraqin da ta dauki fansa kan Amurkan.

Zanga-zangar kin jinin Amurka ya dada yin kamari ne sakamakon wani harin dabbanci da Amurka ta kai kan sansanin dakarun Al'umma ta "Hashdu Sha'abi (Popular Mobilization Forces) inda suka kashe mutun 25 sannan suka raunata mutane sama da 50.

Allah shi kyauta.
Nasir Isa Ali

Comments

Popular posts from this blog

JIRGIN RUWAN ANNABI NUHU DA AMURIKA TA KERA A SHEKARAR 2018

๐๐ˆ๐†๐„๐‘๐ˆ๐€ @60:๐Œ๐”๐‹๐Š๐ˆ๐ ๐’๐Ž๐‰๐€ ๐Œ๐€๐’๐” ๐‡๐€๐‹๐ˆ๐ ๐“๐’๐ˆ๐˜๐€ ๐ƒ๐€ ๐๐€ ๐Š๐ˆ๐‘๐Š๐ˆ

๐™”๐™–๐™ฃ๐™™๐™– ๐™ข๐™–๐™ฏ๐™–๐™ฃ๐™—๐™–๐™ฉ๐™– ๐™ ๐™š ๐™ฉ๐™จ๐™ž๐™ฃ๐™ฉ๐™–๐™ง ๐™ ๐™ฌ๐™–๐™ง๐™ค๐™ง๐™ค๐™ฃ ๐™ง๐™ค๐™—๐™– ๐™จ๐™ช๐™ฃ๐™– ๐™จ๐™–๐™ฎ๐™š๐™ง๐™ฌ๐™– ๐™Ÿ๐™–๐™ข๐™– ๐™–