Cutar Corovirus A Iran: "Damuwa Da Talakawan Kasarsu Da Jami'an Gwamnatin Kasar ta Iran Ke Yi Yasa Manyan Jami'an Gwamnatin Kasar Suka Fi Kamuwa da cutar Coronavirus" -Inji Daraktan WHO

An Bayyana Dalilan Da Yasa Manyan Jami'an Gwamnatin Kasar Iran Ke Kamuwa Da Cutar CoronVirus.

Daraktar kungiyar lafiya ta duniya (WHO) a gabashin duniya Dr.Rechard Brennan ya bayyana dalilan da yasa manyan Jami'an gwamnatin Kasar Iran ke kamuwa da cutar shake makoshi na Korona Bairus(COVID-19.

Daraktan ya bayyana hakan ne a birnin Tehran a lokacin da ya ziyarci Iran,kana ya ziyarci inda ake killace da masu cutar domin ya gane wa idonsa yadda ake kula da lafiyarsu. inda ya yi kira ga kasashen duniya da su yi koyi da kasar ta Iran wajen yakar cutar wannan cuta ta Korona.

Dr.Rechard ya kuma bayyana cewar,Iran ta ciri tuta wajen yin yaki da wannan cutar, sannan yayi kira ga kasashen yankin da duniya baki daya da su yi koyi da Iran wajen yakar wannan cutar.

Ya kara da cewar,Iran tana da ingantattun kayan aiki na zamani masu kyawun gaske,kuma a yankin Asiya kakaf bai ga kayan aiki irin na Iran din ba.

Yace kungiyarsa ta WHO ta bada sharuddan yakar wannan cutar,kuma Iran ce kasar dake bin wannan Ka'idar 100%.

Yace, ya gani da idonsa yadda ma'aikatan lafiya na Iran,tun daga kan ministan lafiya da daraktocinsa da sauran ma'aikatan jinya suke aiki babu-ji-babu-gani wajen kulawa da marasa lafiyarsu.Kuma kusan kowa a Iran ya damu sosai game da wannan halin da aka shiga.Yace, manyan jami'an gwamnatin Iran,malamai da sauransu duk suna shiga aikin domin ganin an ceto rayuwar wadanda suka kamu da cutar,don haka ne ake ganin cutar tana iya kama kowa da kowa koma bayan wasu kasashen da cutar take kama iya talakawansu amma a Iran lamarin ba haka yake ba.Don haka babu mamaki idan jami'in gwamnati ya kamu da cutar,domin su manyan jami'an gwamnatin sun fi kowa damuwa tare da kusantar marasa lafiya domin ceto su daga halin da suka shiga.

A karshe Dr.Rechard ya bayyana cewar,kungiyarsa ta WHO za ta tura jami'an kula da kiwon lafiya zuwa kasashen da ke fama da wannan cutar,kuma Iran tana ciki,kuma yana fatan Iran za ta bai wa Jami'an nata goyon baya 100%.

Comments

Popular posts from this blog

JIRGIN RUWAN ANNABI NUHU DA AMURIKA TA KERA A SHEKARAR 2018

๐๐ˆ๐†๐„๐‘๐ˆ๐€ @60:๐Œ๐”๐‹๐Š๐ˆ๐ ๐’๐Ž๐‰๐€ ๐Œ๐€๐’๐” ๐‡๐€๐‹๐ˆ๐ ๐“๐’๐ˆ๐˜๐€ ๐ƒ๐€ ๐๐€ ๐Š๐ˆ๐‘๐Š๐ˆ

๐™”๐™–๐™ฃ๐™™๐™– ๐™ข๐™–๐™ฏ๐™–๐™ฃ๐™—๐™–๐™ฉ๐™– ๐™ ๐™š ๐™ฉ๐™จ๐™ž๐™ฃ๐™ฉ๐™–๐™ง ๐™ ๐™ฌ๐™–๐™ง๐™ค๐™ง๐™ค๐™ฃ ๐™ง๐™ค๐™—๐™– ๐™จ๐™ช๐™ฃ๐™– ๐™จ๐™–๐™ฎ๐™š๐™ง๐™ฌ๐™– ๐™Ÿ๐™–๐™ข๐™– ๐™–