HIZBULLAH NA SHIRIN TSAYAR DA AL'ƘIYAMAR ISRA'ILA- Dattijan Yahudawa sunyi Gargadi

Hezbolla Da Isra'ila: 'Hezbolla na shirin tsayar da Alkiyamar Israila' -Dattawan Yahudawa Sun gargadi Netanyahu.

Wasu dattawan Yahudawa,Sojoji da 'yan Siyasa,sun bayyana cewa Hezbollah fa na shirin tsayar da Alkiyamar Isra'ila muddin Netanyahu ya takulo yaki da Hezbollah.

Yahudawan su bayyana wa kafofin sadarwar Israila cewar,duk wani yaki da Hezbollah a nan gaba to zai zamo tamkar tashin alkiyama ne ga Isra'ila.

Da farko, tsohon Firayemiyar Israila Mr.Ehud Barak ya bayyana cewar,Hezbollah ta mallaki makami mai linzami mai cin dogon zango,wanda kuma ake iya sarrafa shi da na'ura daga nesa 'Precision-Guided Missile (PGM).

Mr.Ehud Barak ya bayyana cewar,akwai wurare muhimman gaske wanda Hezbollah za su hara idan yaki ya barke tsakaninsu da Israila.

Ya ce za su hari a gine-ginen gwamnati da wasu muhimman wurare kamar ma'aikatar tsaron Israila.

Ya bayyana cewar,hatta ofishin Firayeministan Israila da ginin majalisar kasar (Knesset) ba fa za su tsira daga harin ba.

Shi kuwa shugaban sashin ayyuka na musanman na rundunar sojan Isra'ila,Aharon Halifat ya bayyana cewar,barikokin soja,wuraren adana makamai da tashoshin ruwa na daga cikin inda dakarun Hezbollahi za su kai wa hari.

Yace, ma'aikatar sadarwa da tashoshin sufuri na cikin wuraren da Hezbollah za su kai wa harin manyan makaman mizayil.

Aharon Halifat ya bayyana cewar,ba karamin shiri Hezbollahi ke yi wa Israila ba,kuma yakin zai kasance ne daga ko'ina domin Hezbollah tana Syria,Lebanon da Falastin.Kuma yakin Syria da Iraqi ya kara sa wa Hezbollah sun samu kwarewar yaki sosai.

Ya bayyana cewar,Hedikwatar sojojin Israila,ma'aikatan tsaro da majilisar kasar na cikin sahun gaba a hannun kwamandojin Hezbollah.Don haka duk wani yaki da Hezbolla a nan gaba zai zamo tamkar tashin alkiyama ne ga Israila.

 Mr.Naumi Shamon ya bayyana cewar,tun kafin yakin ya barke,Yahudawa da dama sun firgita,kuma sun tsorata,sun bai wa Hezbolla gari.

Saboda haka dattawan sun yi kira ga mahukuntar Isra'ila na yanzu da su tashi tsaye wajen kara kimtsawa sosai,domin tunkarar wannan bala'in mai tahowa.

Comments

Popular posts from this blog

JIRGIN RUWAN ANNABI NUHU DA AMURIKA TA KERA A SHEKARAR 2018

𝐍𝐈𝐆𝐄𝐑𝐈𝐀 @60:𝐌𝐔𝐋𝐊𝐈𝐍 𝐒𝐎𝐉𝐀 𝐌𝐀𝐒𝐔 𝐇𝐀𝐋𝐈𝐍 𝐓𝐒𝐈𝐘𝐀 𝐃𝐀 𝐍𝐀 𝐊𝐈𝐑𝐊𝐈

𝙔𝙖𝙣𝙙𝙖 𝙢𝙖𝙯𝙖𝙣𝙗𝙖𝙩𝙖 𝙠𝙚 𝙩𝙨𝙞𝙣𝙩𝙖𝙧 𝙠𝙬𝙖𝙧𝙤𝙧𝙤𝙣 𝙧𝙤𝙗𝙖 𝙨𝙪𝙣𝙖 𝙨𝙖𝙮𝙚𝙧𝙬𝙖 𝙟𝙖𝙢𝙖 𝙖