Kasar Iran Za Ta Halba Wasu Taurarin Dan Adam Masu Nisan Kilomita 1000 Daga Doran Kasa.

Iran Za Ta Harba Taurarin Dan Adam Tsawon Kilo Mita 1000 Daga Doron Kasa.

Shugaban hukumar kula da ayyukan sararin samaniya na kasar Iran, Mortadha Barari ya bayyana cewa a cikin shekaru biyu masu zuwa Iran za ta harba wasu taurarin dan adam zuwa sararin samaniya tsawon kilo mita 1000 daga doron kasa.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin Tehran, Barari ya bayyana cewa, baya ga shirin da suke dashi na harba wasu taurarin dan adam a cikin wannan makon mai kamawa, suna da wani shirin na daban tsakanin shekara guda zuwa shekaru biyu masu zuwa.

Ya bayyana cewa wannan yana daga cikin babban ci gaban da suka samu a bangaren ilimin kimiyya, wanda ya mayar da Iran din ta zama ta daya ayankin gabas ta tsakiya wajen harba tauraron dan adam, kamar yadda kuma ita ce ta tara a duniya a halin yanzu a wannan fage.

Ya ce kammala aikin shekaru biyu masu zuwa, Iran din za ta harba wasu taurarin dan adam tsawon kilo mita dubu 36 daga doron kasa.

Comments

Popular posts from this blog

JIRGIN RUWAN ANNABI NUHU DA AMURIKA TA KERA A SHEKARAR 2018

๐๐ˆ๐†๐„๐‘๐ˆ๐€ @60:๐Œ๐”๐‹๐Š๐ˆ๐ ๐’๐Ž๐‰๐€ ๐Œ๐€๐’๐” ๐‡๐€๐‹๐ˆ๐ ๐“๐’๐ˆ๐˜๐€ ๐ƒ๐€ ๐๐€ ๐Š๐ˆ๐‘๐Š๐ˆ

๐™”๐™–๐™ฃ๐™™๐™– ๐™ข๐™–๐™ฏ๐™–๐™ฃ๐™—๐™–๐™ฉ๐™– ๐™ ๐™š ๐™ฉ๐™จ๐™ž๐™ฃ๐™ฉ๐™–๐™ง ๐™ ๐™ฌ๐™–๐™ง๐™ค๐™ง๐™ค๐™ฃ ๐™ง๐™ค๐™—๐™– ๐™จ๐™ช๐™ฃ๐™– ๐™จ๐™–๐™ฎ๐™š๐™ง๐™ฌ๐™– ๐™Ÿ๐™–๐™ข๐™– ๐™–