Matsalar Tsaro a Najeriya: Shaikh Bala Lau Ya Yi Kira Da A Koma Ga Allah Kurum.

"Komawa Zuwa ga Allah Shi ne Maganin Fitinun Ƙasar Nijeriya" – Sheikh Bala Lau.

Shugaban ƙungiyar IZALA na tarayyar Nijeriya, Ash-Sheikh Dr Imam Abdullahi Bala Lau ya bayyana cewa komawa ga Allah Maɗaukakin Sarki ne maganin fitintinu da suka addabi ƙasar Nijeriya.

Sheik Bala Lau ya bayyana hakan ne a yayin da yake zantawa da 'yan jarida a gidan sa dake Yola.

Bala Lau yace a duk lokacin da annoba, ko bala'i ya samu mutum, to abu na farko shine ya komawa Allah. Yace dole ne sai mutane sun fahimci cewa babu mutum da zai iya yaye fitina ko bala'i idan ya taso wa al' umma face Allah.

"Idan ka dauki kasar nan tun daga zamanin su Sardauna, wadanda suka san tarihi sun san irin matsaloli da su sardauna suka fiskanta duk da ƙoƙarin su da adalcin su mutane a wancan lokacin suna gani tamkar sun kasa, wanda hakan ne ya haifar da rayuwar su ta tafi ta wannan hanya

"Saboda haka, kowani zamani da irin jarrabawa da mutane suke fiskanta, daga zamanin 'yan siyasa har sojoji. Amma idan za'a mayar da al'amarin zuwa ga Allah, to Allah yace zai samar mana mafita kuma zai buɗa mana ƙofofin rahamar Sa." inji Sheikh Bala Lau.

Shehin malamin yace abunda yake faruwa na tashin hankali na Boko Haram da sace sacen mutane jarabawa ne da Allah ya jarrabi al'umman wannan ƙasa dashi. Saboda haka yace komawa ga Allah Shine mafita.

Sheikh yace: "sannan hukumomi akwai hakki a kan su. Yace dole ne hukumomi su kare rayuka da dukiyoyin al'umma. Sayyidna Umar yana cewa idan wata dabba tayi tuntube tun daga Madina har zuwa ƙasar Iraqi sai an tambaye shi. Kenan kowa yayi rayuwa cikin tsaro da aminci hakki ne a wuyan shugaba.

"sannan masu ta'addanci, ka lura da su. Ta'addanci bata da addini. Zaka samu akwai a cikin musulmai kuma akwai a cikin waɗanda ba musulmai ba. Saboda haka a daina keɓance wata addini ana jifan ta da ta'addanci a Nijeriya." Inji Shehin malamin.

Da yake maganna akan zamantakewa tsakanin musulmi da wanda ba musulmi ba, Dr. Bala Lau yace musulunci shine addini mafi son zaman lafiya a duniya. Yace wannan yasa musulunci bai yadda da ɗaukan makami akan wanda ba musulmi ba haka kawai. Yace akwai bukatar waɗanda ba musulmi ba su san wannan. Kada abu da ya faru a garesu su jefi musulmi da laifin aikata shi.

Comments

Popular posts from this blog

JIRGIN RUWAN ANNABI NUHU DA AMURIKA TA KERA A SHEKARAR 2018

𝐍𝐈𝐆𝐄𝐑𝐈𝐀 @60:𝐌𝐔𝐋𝐊𝐈𝐍 𝐒𝐎𝐉𝐀 𝐌𝐀𝐒𝐔 𝐇𝐀𝐋𝐈𝐍 𝐓𝐒𝐈𝐘𝐀 𝐃𝐀 𝐍𝐀 𝐊𝐈𝐑𝐊𝐈

𝙔𝙖𝙣𝙙𝙖 𝙢𝙖𝙯𝙖𝙣𝙗𝙖𝙩𝙖 𝙠𝙚 𝙩𝙨𝙞𝙣𝙩𝙖𝙧 𝙠𝙬𝙖𝙧𝙤𝙧𝙤𝙣 𝙧𝙤𝙗𝙖 𝙨𝙪𝙣𝙖 𝙨𝙖𝙮𝙚𝙧𝙬𝙖 𝙟𝙖𝙢𝙖 𝙖