Ta Yafe Mai Sadakinta Bayan Ya Yi Mata Alkawalin Ba Zai Yi Mata Kishiya Ba Har Abada.
Alkawalin Cewa Ba Zai Yi Wa Amaryarsa Kishiya Ba,Ya Ja Masa Tagomashin Yafe Sadakin Aurensa Daga Matar Da Zai Aura.
Wata amarya Ta Yafe Wa Ango Sadakinta, bayan angon ya yi alkawarin ba zai yi mata kishiya ba har su kwanta daka.
Wata mata mai suna Aishat Busari ta wallafo cewa, wata amarya ta ce ta yafe sadakin aurenta ga angonta,amma sai dai ta ce angon ya yi mata alkawari a bainar jama’a cewa ba zai yi mata kishiya ba.
Wannan dai ya faru a Offa, jihar Kwara, inda amaryar mai suna Fatima Babawale ta ce ta yafe sadakinta a daurin aurenta da aka yi ranar 15 ga watan Fabrairun 2020.
A musulunce sadaki na daya daga cikin sharuddan aure, amma ya danganta da yarjejeniyar ango da amarya a kan abin da za a bayar a matsayin sadakin auren.
Yadda abin ya faru shi ne; a lokacin daurin auren Muhammad Adebayo da Fatima Babawale, ranar Asabar 15 ga watan Fabrairu, 2020, Alfa ya bukaci Muhammad ya fito ya biya sadaki, sannan kuma ya tambayeshi wane irin sadaki zai bayar, Muhammad na shirin bayar da sadakin na kudi, sai Fatima ta tashi tsaye ta cewa Muhammad kada ya biya sadakin, daya daga cikin mutanen wajen ya tambayeta menene take so, sai ta ce tana so Muhammad yayi mata alkawarin ba zai yi mata kishiya ba a bainar jama’a hakan shine matsayin sadaki a wajenta, Muhammad yayi mamaki matuka, saboda ba su yi wannan maganar da ita ba kafin ranar daurin auren.
Muhammad yaje ya dan tattauna da iyayenshi na dan mintuna, suka ce mishi yayi abin da matar tashi ta bukata.
Sai ya dauki lasifika, yayi mata wannan alkawari a gaban bainar jama'ar da suka taru daurin auren nasu.
Duba da yadda ake samun matsala har ta kai ga an rasa rai ga mazajen da ba su yi irin wannan alkalin ba ga matayensu,A ganinku sai wani dalili ya sa shi kara auren bisa hukuntawar ubangiji a hasashenku wane mataki matar ita kuma za ta iya dauka musamman da ta shi yayi alkawalin nan a gaban Mutane?

Comments
Post a Comment