ABIN LURA: game da yaƙi da CORONAVIRUS

Abin lura game da yaki da cutar Corona Virus

Daga Abdulmumin Giwa

Da farko zan ba da hakurin yin rubutun da ingausa.

Problem din shine babu test kits da za a gwada mutane a kare rayuwarsu. Na ji an ce an samu gwada kimani mutane 700 kacal a Nigeria daga cikin mutane miliyan 200.

Akwai tsarin kiwon lafiya da ake cewa Preventive Healthcare sannan kuma akwai Curative healthcare. Shi Preventive Healthcare aikin lafiya ne na kariya daga kamuwa da ga cuta. Za a kareka daga kamuwa da shi ta hanyoyin aikin lafiya daban daban. In an lura za a ga cewa gwamnati ba ta komai a wannan sashi game da wannan annoba ta Corona Virus. Kamata ya yi ana gwada mutane ana kebe wadanda aka samu don warkar dasu kafin ya tumbatsa. Kuma kamata ya yi a rika feshi a wuraren jama'a kamar kasuwanni, wuraren ibada, malls, unguwanni da sauransu. Amma ba a komai ta wannan fannin.

A daya hannun kuma, shi Curative Healthcare tsarin lafiya ne ba warkar da wanda ya kamu da cuta. Wannan bangaren shine gwamnati ke nuna ta damu da shi alhali ba ta da kayan aiki musamman ventilators da respiratory machines. Babu isassun asibitoci da ake cewa ICU wato Intensive Care Units wadanda su ake bukata a wannan irin yanayi. Duk a fadin Nigeria ba su kai guda Dari hudu ba wadanda ba za su iya kulawa da dubban mutane ba idan har aka yi sake cutar ta barke.

Saboda haka Preventive Healthcare dinnan shi ne muhimmi a halin da ake ciki domin hana yaduwan cutar. Kuma hana fita na daga ciki amma tare da baiwa jama'a walwalan abinci da sauransu don su zauna a gida har a gama yaki da cutar. In sun zauna a gida sai a bi ko ina a feshe da maganin kashe cutar. Amma a halin yanzu gwamnati ba ta damu da shi ba.

Saboda haka kawai mu kare kawukanmu ta hanyan bin shawarwarin jami'an lafiya. Lallai gwamnati ba ta nuna shirin yaki da wannan cuta ba.

Comments

Popular posts from this blog

JIRGIN RUWAN ANNABI NUHU DA AMURIKA TA KERA A SHEKARAR 2018

𝐍𝐈𝐆𝐄𝐑𝐈𝐀 @60:𝐌𝐔𝐋𝐊𝐈𝐍 𝐒𝐎𝐉𝐀 𝐌𝐀𝐒𝐔 𝐇𝐀𝐋𝐈𝐍 𝐓𝐒𝐈𝐘𝐀 𝐃𝐀 𝐍𝐀 𝐊𝐈𝐑𝐊𝐈

𝙔𝙖𝙣𝙙𝙖 𝙢𝙖𝙯𝙖𝙣𝙗𝙖𝙩𝙖 𝙠𝙚 𝙩𝙨𝙞𝙣𝙩𝙖𝙧 𝙠𝙬𝙖𝙧𝙤𝙧𝙤𝙣 𝙧𝙤𝙗𝙖 𝙨𝙪𝙣𝙖 𝙨𝙖𝙮𝙚𝙧𝙬𝙖 𝙟𝙖𝙢𝙖 𝙖