ASALIN CUTAR CORONA VIRUS DA KUMA YANDA ZA'A KAUCE MATA

Hanyoyin Riga-Kafin Kamuwa Da Cutar Koronabairus

Daga Dakta Shu’aibu Musa

Cutar Koronabairus wani nau’in cuta ne da kwayoyin cuta da bairus ke kawowa dangin kwayoyin cuta da ke janyo cutar mura ko mashako da wasu cututtuka masu tsanani. COVID-19 shi ne sunan da aka sa wa sabuwar kwayar cutar da ke janyo cutar Korona da ta zama annoba. A yanzu tana neman ta mamaye duniya. An fara gano wannan kwayar cutar ne a 2019 a yankin Wuhan na kasar Sin (China).

Cutar Korona, cututtuka ne da ake dauka daga dabbobi. A can baya an yi wasu nau’o’in cututuka da Korona bairus ke kawowa, kamar cutar murar tsuntsaye da ake dauka daga tsuntsaye da cutar haukan shanu da sauransu. Akwai ma cututtuka da dama da Korona bairus ke kawowa da ke shafar dabbobi ne kawai, amma ba su riga sun fara shafar mutane ba.

Manyan alamomin wannan ciwon Korona din sun hada da:- Zazzabi da tari da numfashi sama-sama, ko daukewar numfashi. In cutar ta tsananta, takan zamanto tamkar ciwon ‘pneumonia’ (nimoniya), ko ciwon koda, kuma takan yi sanadiyyar mutuwa.

Hanyoyin kariya daga kamuwa da wannan ciwon sun hada da yawaita wanke hannu da rufe baki da hanci a yayin tari ko atishawa da dafa nama ko kwai ya dafu sosai. Sai kuma nisantar duk wani da ke nuna alamun mura ko tari.

Wani muhimmin abu kuma shi ne a ci gaba da karin neman sani dangane da wannan cutar ta ingantattun hanyoyi da guje wa jita-jita da labarun karya da wadanda ba su da sani kan lamarin ke yadawa.

Yawancin wadanda suka kamu da wannan cutar ba su yin ciwo mai tsanani, kuma sukan warke daga cutar, amma wasu kuwa cutar takan tsananta sosai. Dole ka kula da lafiyar jikinka, kuma ka kare sauran mutane daga kamuwa ta hanyar daukar wadannan matakan:

Wanke hannaye a kai, a kai da ruwa da sabulu ko ruwan sabulu da ake tsaftace hannu da shi da ake kira ‘hand sanitizer’ a Turance.

Dalilin yawaita wanke hannu shi ne cewa yin hakan yakan kashe kwayoyin cuta da ke hannun mutum.

Ka nisanci duk wani da ke tari ko yawan atishawa da kimanin tsawon mita daya ko kafa uku.

Dalilin yin haka kuwa shi ne don duk lokacin da mutum ya yi tari ko atishawa yakan watsa fetsin ruwa da ka iya zama yana dauke da kwayoyin cuta. In ka kusance shi kana iya shakar wadannan kwayoyin cutar, ciki kuwa har da Korona bairus muddin mutumin yana dauke da ita.

Ka daina yawan kai hannunka zuwa ido ko hanci ko baki. Dalili kuwa shi ne don hannayenka sukan tabi wurare da daman gaske, kuma ta hakan suna iya kwasar kwayoyin cuta, kamar yadda ya wajaba a daina yin musabaha hannu da hannu, domin muddin hannayenka sun kwashi wadannan kwayoyin cutar, kana iya kai su idonka ko hancinka ko bakinka. Daga nan kuma wadannan kwayoyin cutar suna iya shiga jikinka, kuma su sa ka ciwo.

Dole kai da wadanda ke kusa da kai su koyi tarbiyyar rufe baki da hanci a yayin tari ko atishawa a kowane lokaci da kyalle ko takardar da ake kira ‘tisuue paper’ a Turance. Daga nan sai a yar da waccan kyallen ko takardar ‘tissue’ din.

A nan dalili kuwa shi ne cutar na yaduwa ne ta hanyar shakar numfashi, kuma muddin ba a rinka rufe baki da hanci ba wurin tari ko atishawa ana iya yada wannan cutar cikin sauki. Dole kuma a daina yin kaki ana tofarwa ko’ina ko tofar da miyau ta ko’ina haka kawai.

Da zarar mutum ya fara jin zazzabi ko ya fara tari ko samun daukewar numfashi, dole ya garzaya asibiti don neman taimako. Daga nan kuma dole ya takaita zirga-zirga da kadaita hulda da mutane ko a gidansa ne, gudun kar ya yada wa wasu. Matakan kariya ga mutanen da suke zama ko suka zo cikin kasa da kwanaki 14 daga inda cutar ta riga ta barke kuwa, ya hada da ba Hukumomin kiwon lafiya matakan da suke dauka don ganin ciwon nan bai yadu ba.

Wadannan matakai sun hada da zama a gida don gudun cudanya da wadanda suke dauke da wannan cutar. Hakan na nufin kaurace wa duk inda ake taruwa na jam’i, kamar kasuwanni, makarantu, masallatai, coci-coci da wuraren biki ko taron kallon kwallo da sauransu.

Hukumomi kuma suna iya hana shige da fice daga kasa ta hanyar shigowa da wannan bairus din. Wasu kasashe sun riga sun rufe bodarsu, musamman daga mutanen da suka fito daga kasashen da annobar ta fi shafa.

Yin haka na wani tsawon lokaci zai sa a iya magance yaduwar ciwon cikin hanzari.

Da zarar ka fara jin rashin lafiya, musamman mura ko zazzabi, ka hanzarta zuwa asibiti don a duba lafiyarka.

Comments

Popular posts from this blog

JIRGIN RUWAN ANNABI NUHU DA AMURIKA TA KERA A SHEKARAR 2018

๐๐ˆ๐†๐„๐‘๐ˆ๐€ @60:๐Œ๐”๐‹๐Š๐ˆ๐ ๐’๐Ž๐‰๐€ ๐Œ๐€๐’๐” ๐‡๐€๐‹๐ˆ๐ ๐“๐’๐ˆ๐˜๐€ ๐ƒ๐€ ๐๐€ ๐Š๐ˆ๐‘๐Š๐ˆ

๐™”๐™–๐™ฃ๐™™๐™– ๐™ข๐™–๐™ฏ๐™–๐™ฃ๐™—๐™–๐™ฉ๐™– ๐™ ๐™š ๐™ฉ๐™จ๐™ž๐™ฃ๐™ฉ๐™–๐™ง ๐™ ๐™ฌ๐™–๐™ง๐™ค๐™ง๐™ค๐™ฃ ๐™ง๐™ค๐™—๐™– ๐™จ๐™ช๐™ฃ๐™– ๐™จ๐™–๐™ฎ๐™š๐™ง๐™ฌ๐™– ๐™Ÿ๐™–๐™ข๐™– ๐™–