FASHEWAR SINADARAI A LABANON KO TARIHI ZAI MAIMAITA KANSA NE? daga Awwal Bauchi
FASHEWAR SINADARAI A LABANON...KO TARIHI NA SHIRIN MAIMATA KANSA NE?
A halin yanzu dai dukkanin idanuwa sun koma ƙasar Labanon sakamakon fashewar da ta faru a tashar bakin ruwa ta Beirut, babban birnin ƙasar, wacce ta yi sanadiyyar mutuwa da raunana daruruwan mutane. A daidai lokacin da ƙasashen duniya suke ta nuna alhininsu kan wannan lamari da kuma aikewa ko kuma alƙawarin aikewa da kayayyakin agaji, gwamnatin ƙasar dai ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbabin faruwar hakan da kuma alƙawarin hukunta duk waɗanda suke da hannu ciki, haka nan ƙungiyoyi daban-daban na ƙasar suna ci gaba da Allah wadai da faruwar hakan duk da cewa wasu kuma tamkar wata dama ce ta samu don cimma tsohuwar ‘baƙar’ aniyarsu a kan ƙasar.
Tambayar da dai take yawo a halin yanzu ita ce shin ko tarihi ne ya ke ƙoƙarin maimaita kansa a Labanon ɗin? Shin waye zai amfana da wannan fashewar?
Idan dai ana iya tunawa shekaru 15 da suka gabata ƙasar Labanon ɗin ta shiga shigen irin wannan yanayin, sakamakon kisan gillan da aka yi wa tsohon firayi ministan ƙasar, Rafiƙ Hariri, wanda daga ƙarshe dai ta bayyana cewar an yi wannan kisan ne don cimma wata manufa da aka gagara cimma ta da ƙarfin tuwo: ficewar sojojin Siriya daga Labanon, kwance ɗamarar Hizbullah da kuma tabbatar da tsaron ‘Isra’ila. A wannan lokacin dai, ‘yan ƙasar sun ta faɗa da junansu daga ƙarshe dai babu abin da hakan ya haifar musu in ban da lalata ƙasar su.
Hakan ne ma ta sanya wasu tambayar cewa an ya wannan fashewar ta ranar Talatar da ta gabata (04/08/2020) ba wani sabon ƙoƙari da kuma makirci ne, irin na kisan gillan da aka yi wa Haririn, don cimma wancar manufar ba kuwa ganin cewa har ya zuwa yanzu ba a cimma wasu daga cikin abubuwan da aka so cimmawa ɗin ba? To a haƙiƙanin gaskiya ba abu ne da za a iya kore shi ba, musamman idan aka yi la’akari da irin nasarorin da ƙungiyar Hizbullah ɗin (wacce dukkan alamu suna nuni da cewa ita ce ake hari) ta samu kuma take ci gaba da samu a yaƙin da ta ke yi a Siriya da kuma irin ƙarfin da ta ke ƙara yi wanda hakan ke ci gaba da zama barazana ga Isra’ila (kamar yadda muka yi ishara da shi a wani rubutu a baya). Wato daidai da irin abin da ya faru lokacin da aka kashe Haririn, wanda a lokacin Hizbullah ta ƙara samun ƙarfi bayan ta tilasta wa Isra’ila ficewa daga kudancin Labanon a 2000 bugu da ƙari kan nasarorin da ta dinga samu a fagen siyasar cikin gida.
Wani lamari kuma da ke nuni da alamun makirci cikin wannan lamarin shi ne irin yadda wasu kafafen watsa labaran larabawa musamman waɗanda suke da alaƙa da Saudiyya (Al-Hadath da Al-Arabiyya) suke ta ƙoƙarin jingina faruwar fashewar ga ƙungiyar ta Hizbullah, a daidai lokacin da dukkanin cibiyoyin gwamnati da na tsaro na ƙasar Labanon ɗin suke nuni da akasin hakan, kai wasu ma suke nuni da yiyuwar ‘zagon ƙasa’ ne sakamakon yadda wasu cibiyoyin da abin ya shafa suka ta nuna kunnen uwar shegu ga buƙatar da hukumomi, musamman hukumar ‘Kwastan’ ta tashar bakin ruwan, suka dinga gabatar musu na ɗaukar matakan da suka dace wajen kwashe wannan sinadarin na ‘ammonium nitrate’ da aka ce ya kai ton 2,750 da aka ƙwace daga wani jirgin ruwan ƙasar Moldova da ya iso tashar daga ƙasar Georgia a hanyarsa ta zuwa ƙasar Mozambique a watan Satumban 2013 amma hukumomin da abin ya shafa suka yi kunnen uwar shegu da wannan buƙata, duk kuwa da hatsarin da ke tattare da ci gaba da ajiye wannan sinadari mai tsananin fashewa a wajen, kai ka ce daman kamar akwai wani abin da ake jira ne.
Dukkanin wannan dai hasashe ne, ko shakka babu cikin kwanaki masu zuwa abubuwa za su ci gaba da bayyana sakamakon binciken da gwamnatin ƙasar ta ke ci gaba da yi. To sai dai wani abu da ke da muhimmanci a nan wanda kuma babu komai kashin kokwanto cikinsa shi ne cewa lalle ko shakka babu Isra’ila da Amurka za su yi amfani da wannan damar ta fashewar wannan sinadarin don cimma tsohon burinsu a ƙasar Labanon idan ma har mun kore yiyuwar hannunsu a ciki kenan da kuma yarda da cewa lamarin ya faru ne haka kawai ba wai an tsara shi ba ne.
Dubi cikin fagen siyasar ƙasar Labanon cikin ‘yan watannin da suka gabata kama daga lokacin da aka kafa sabuwar gwamnati Hassan Diab, wadda a fili wasu ƙasashen larabawa da na yammaci ba su so hakan ba, saboda abin da suka bayyana da cewa gwamnatin ta Hizbullah ce, har zuwa ga irin matsin lambar da suka dinga yi wa gwamnatin da ƙirƙiro zanga-zangogin jama’a da matsin lamba na tattalin arziki duk dai da nufin kifar da gwamnati, zuwa ga takunkumin dokar Caeser da Amurkan ta sanya wa Siriya wanda ta wani ɓangare zai iya shafan tattalin arzikin Labanon, kwatsam sai kuma ga wannan fashewar ta tashar bakin ruwan na Beirut, wacce ta nan ne ake shigo da kashi 70% na dukkanin kayayyakin da ake shigowa da su ƙasar don amfani al’umma, don haka a fili yake cewa hakan zai yi gagarumin tasiri ga tattalin arzikin ƙasar.
Daga dukkan alamu dukkanin waɗannan abubuwan an tsara su ne don share fagen haifar da wani sabon yanayi da nufin cimma wancan manufar dai guda ɗaya tilo: kwance ɗamarar ƙungiyar Hizbullah ko kuma alal aƙalla raunana ta a fagen siyasa da kuma na soji. Don kuwa ko shakka babu Amurka da waɗannan ƙawayen na ta za su yi ƙoƙari wajen shigowa da dukkan ƙarfinsu, da sunan ƙara ƙarfafa tattalin arzikin Labanon, tabbatar da tsaron ƙasar da dai sauransu, kamar yadda suka yi bayan kisan gillan da aka yi wa Hariri, don cimma manufofinsu.
To sai dai kuma idan abin a wannan ɓangaren mu sake komawa cikin tarihi ɗin ne, muna iya cewa dukkanin alamu suna nuni da cewa da wuya su iya cimma wannan manufar ta su, kamar yadda suka gaza cimmawa a baya, bisa la’akari da irin ƙwarewar da Hizbullah ɗin take da ita wajen magance irin waɗannan matsaloli da kuma makirce-makircen da ake ƙulla mata, kamar yadda suka yi bayan kisan gillan da aka yi wa Haririn da kuma irin yadda ‘duniya’ ta yi caa a kan su.hrtvnetwork.ng@gmail.com
Comments
Post a Comment