HUKUNCIN KISA DA KOTUN MUSULINCI DAKE KANO TA YANKEMA WANI MATASHI SHARIF AMINU MI ZAI BIYO BAYA?

 HUKUNCIN KISA DA ALKALIN KOTUN SHARI'AR MUSULINCI DA KE KANO YA YANKE MA WANI MATASHI SHARIF AMINU- Wace dama ta rage masa yanzu kafin wa'adin wata ɗaya. 

Bayan da babbar Kotun Shari'ar Musulunci ta yanke wa mawakin nan Aminu Yahaya Sharif hukuncin kisa kan laifin aikata sabo na zagin Manzon Allah SAW, mutane da dama za su so su san mene ne abu na gaba kan zartar da wannan hukunci.

A cewar alkalin da ya yanke hukuncin Mai Shari'a Aliyu Mohammed Kani, mawaƙin yana da kwana 30 don daukaka kara.

Me zai faru a Kotun Ɗaukaka Ƙarar?

Barista Musa Salihu lauya ne a Abuja babban birnin kasar, ya ce abin da zai faru idan an je Kotun Daukaka Kara shi ne za a yi amfani da dokokin Najeriya ne ba na Shari'ar Musulunci ba.

Ya ce: ''Idan Yahaya ya yanke shawarar daukaka kara, to zai samu sauki inda ba za a yi masa hukunci da Shari'ar Musulunci ba sai na dokokin Najeriya wadanda za su iya sauya hukuncin da Kotun Shari'a ta yanke masa.'' 

Wacce dama ta rage wa mawaƙin?

Baba Jibo Ibrahim shi ne mai magana da yawun kotunan jihar Kano. Ya shaida wa BBC cewa ba zai yiwu a rataye Yahaya a nan kusa ba, saboda har yanzu wani mutum Abdulazeez Inyass da aka yanke masa irin wannan hukuncin yana kulle ba a zartar masa ba.

''Ba za a zartar da hukuncin ba nan kusa saboda mawakin na da damar daukaka kara, kuma ko da za a zartar din ma dole sai gwamna ya sanya hannu.''

Shi ma mai magana da yawun gidajen yarin Kano Musbahu Lawal haka ya ce kan batun Aminu.

"Ana bukatar gwamna ya sanya hannu kafin a zartar da hukuncin kisa, kuma gwamnonin ba su faye sa hannun ba, don haka masu irin wadannan laifukan suna tare da mu.''

Me ake cewa a shafukan sada zumunta?

A Najeriyar dai mafi yawan mutane hukuncin ya yi musu dadi yayin da wasu kuwa ba su ji daɗin hukuncin ba, kamar yadda suka yi ta bayyana wa a shafukan sada zumunta.

Wannan ba abin mamaki ba ne idan aka duba cewa Najeriya cike take da mabiya addinai da ƙabilu daban-daban, hakan ya bayyana ƙarara a dandalin Twitter.

Wanda ya jagoranci zanga-zangar neman a hukunta mawaƙin mai suna Yahaya Aminu Sharif, Idris Ibrahim ya shaida wa BBC cewa "mun ji daɗin hukuncin kuma izina ce ga sauran jama'a wadanda ke son bin hanya irinta Yahaya"

Yadda tattaunawar take gudana

Da dama daga cikin ra'ayoyin da jama'a suka bayyana na cin zarafi ne ga addinai da kuma wasu abubuwa masu tsarki, waɗanda BBC ba za ta iya wallafawa ba.

Maudu'ai irin su #Islam da #Kano da #Shari'a da #Mohammed (Annabi Muhammad S.A.W.) da #BokoHaram da #Blasphemy (saɓo) da #Christians (Kiristoci) da #Quran da #Religion (addini) duka suna cikin abubuwa da ake tattaunawa a kansu a Twitter.

An yi amfani da maudu'in #Islam sau fiye da 120,000 - mafi yawa a cikinsu - sai #Blasphemy fiye da 31,000, #Kano fiye da 35,000, Muhammad fiye da 41,000, #Qur'an fiye da 32,000, #Sharia fiye da 16,000.

Kazalika kalmar 'Blasphemy' ce ta biyar a matsayin wadda 'yan Najeriya suka fi neman ƙarin bayani a kanta a shafin Google Trend na matambayi-ba-ya-ɓata, inda aka nemi ƙarin bayani a kanta sau fiye da 5,000.

Kalmar blasphemy tana nufin furta kalaman ɓatanci ga wani abu na addini da ake girmamawa ko kuma saɓo a taƙaice, wadda da ita kafafen yaɗa labarai na Ingilishi suka riƙa bayar da rahoton hukuncin kisan.

Jihohi 12 ne ke amfani da tsarin Shari'ar Musulunci a Najeriya kuma Musulumai kawai ake yi wa hukunci a kotunanta.

Tsarin Shari'a na da na sa Kotun Daukaka Karar da ke kula da mugayen laifuka da na saɓani na yau da kullum da suka shafi Musulmai, kuma Musulmai na da damar daukaka karar hukuncin da Kotun Shari'a ta yanke zuwa kotunan tsarin mulkin Najeriya na Daukaka Kara da Kotun Koli.

Alƙalan kotunan shari'a da ake kira Alkalai suna da ilimin addinin Musulunci da na zamani.

Hukuncin zagin Manzon Allah

Manyan malaman Musulunci sun yi ittifaki cewa zagin Manzon Allah da wulakanta shi da ci masa zarafi zunubi ne mai girma kwarai da gaske, sannan wanda ya aikata hakan ya bar Musulunci, wanda ya bar addinin kuma hukuncinsa shi ne kisa.

Dr Ibrahim Disina babban malamin addinin Msuulunci ne a Najeriya, ya kuma ce akwai hidisin Imam Muslim wanda Abdullahi Ibn Mas'ud ya ruwaito Manzon Allah SAW na cewa: ''Duk wanda ya bar addininsa ku kashe shi.''

Malamin ya ce dukkan malaman Musulunci sun yarda tare da tsayawa a kan wannan maganar.

Mece ce ridda?

Ridda ita ce fita daga Musulunci bayan kasantuwar mutum Musulmi.

Hakan na faruwa ne ta hanyar aikata abubuwan da shari'a ta ce suna fitar da mutum daga Musulunci, kamar shirka ko zagin Allah ko zagin Manzon Allah SAW ko yi wa Allah karya ko wulakanta Al-kur'ani ko yin sujjada ga wanda ba a Allah ba, kamar yadda Dr Disina ya bayyana.

"Hukuncin ridda shi ne kisa," in ji Dr Disina, yana mai cewa Mazon Allah S.A.W. ya ce "duk wanda ya sauya addininsa ku kashe shi, a cikin hadisin da Imamu Muslim ya rawaito daga Abdullah bn Mas'ud".

Daga cikin irin abubuwan da ke jawo ridda akwai aibata Manzon Allah da wulaƙanta shi da zaginsa, in ji Dr. Disina.

"Duk wanda ya zagi Manzon Allah da gangan ko a cikin wasa ya bar Musulunci. Wannan shi ne matsayin dukkan malaman Musulunci, har ma ya shiga ciikin abin da suke kira ijma'i wato ittifaƙi.hrtvnetwork.ng@gmail.com

"Wani malami mai suna Ishaq Ibn Rahauyah ya ce duk mutumin da ya zagi Allah ko ya musanta wani abin da Allah ya saukar to ya fita daga Musulunci ko da yana ci gab da amsa sunan Musulmi.

Comments

Popular posts from this blog

JIRGIN RUWAN ANNABI NUHU DA AMURIKA TA KERA A SHEKARAR 2018

𝐍𝐈𝐆𝐄𝐑𝐈𝐀 @60:𝐌𝐔𝐋𝐊𝐈𝐍 𝐒𝐎𝐉𝐀 𝐌𝐀𝐒𝐔 𝐇𝐀𝐋𝐈𝐍 𝐓𝐒𝐈𝐘𝐀 𝐃𝐀 𝐍𝐀 𝐊𝐈𝐑𝐊𝐈

𝙔𝙖𝙣𝙙𝙖 𝙢𝙖𝙯𝙖𝙣𝙗𝙖𝙩𝙖 𝙠𝙚 𝙩𝙨𝙞𝙣𝙩𝙖𝙧 𝙠𝙬𝙖𝙧𝙤𝙧𝙤𝙣 𝙧𝙤𝙗𝙖 𝙨𝙪𝙣𝙖 𝙨𝙖𝙮𝙚𝙧𝙬𝙖 𝙟𝙖𝙢𝙖 𝙖