YANDA AKA KAMA ƊAN CIA JAMSHID SHARMAHD-

Nasir Isa Ali
-
Jamshid Sharmahd (Dan CIA)
Ya bar jihar California inda yake zaune, kuma daga nan yake jagorantar kungiyarsa ta 'Thunder' zuwa Dubai domin haduwa da abokan kasuwancinsa.
Daga nan bamu kara jin duriyar wayarsa ba,sai daga baya. Amma bayanan farko sun nuna cewar,an bibiyi wayar tasa ta hanyar wani tauraron dan adam,sai aka gano cewar,daga Dubai aka tsallaka da shi zuwa kasar Oman,kana aka bi ta hanyar ruwa zuwa Iran da shi.
-
Mu mun san cewar Sharmahd ya tsara cewar,daga Dubai zai wuce zuwa kasar India ne domin yin cininkin kayayyakin kamfaninsa na komfuta. Lokacin da aka fada mana cewar an shigar da shi cikin wata mota mai duhu kuma an tsallaka da shi zuwa Oman sai hankalin mu ya tashi sosai. Sai daga baya muka gan shi an daure masa fuska da bakin kyalle ana nuna shi kan talbijin din Iran cewar 'jami'an leken asirin Iran sun yi Ram da shi.
-
Lallai baban namu ya bugo mana waya daga wani hotel dake cikin filin saukar jiragen sama na Dubai,kana yace mana yana shirin tashi zuwa India,amma kuma sai aka ce damu wai ya hau mota zuwa Oman,lallai tun daga nan muka fara jin cewar akwai abinda ke faruwa da Abban namu. Wannan ya dada nuna mana yadda Iran ke sarrafa kasashen Larabawa wajen gudanar da Irin wannan ayyukan nata na leken asiri.
-
Abban namu yana da jinsiyya guda biyu,shi dan kasashen Iran da Jamus ne kuma shekarunsa 65 a duniya,kuma tun bayan hambarar da gwamnatin Shah yake aikin yada labarai da kungiyar Thunder.
Amma su kuma jami'an leken asirin Iran karkashin Mahmud Alawi sun bayyana cewar sun kama shi ne a Tajikistan.
Don haka muna kira ga kungiyoyi da gwamnatocin Demokuradoya na duniya da su tashi tsaye wajen ceto mana Abban namu.
--
Wannan wani bamgare ne na wata hira wacce 'Da ga dan CIA Sharmahd Mr. Shayan Sharmahd
 ya yi da wasu kafofin yada labarai na yammacin turai.
-
Amma insha Allahu ta'ala Jaridar Ku mai farin jini,Jaridar mus
YANDA IRAN TA CAFKE ƊAN LEƘEN ASIRIN CIAlunci wato Al-Mizan zata kawo muku sahihi kuma cikakken bayani game da yadda aka cafke wanna. MUFSIDIN bawan insha Allahu.
Ku dai ku cigaba da bibiyar Al-Mizan.
-
Nasir Isa Ali.

Comments

Popular posts from this blog

JIRGIN RUWAN ANNABI NUHU DA AMURIKA TA KERA A SHEKARAR 2018

𝐍𝐈𝐆𝐄𝐑𝐈𝐀 @60:𝐌𝐔𝐋𝐊𝐈𝐍 𝐒𝐎𝐉𝐀 𝐌𝐀𝐒𝐔 𝐇𝐀𝐋𝐈𝐍 𝐓𝐒𝐈𝐘𝐀 𝐃𝐀 𝐍𝐀 𝐊𝐈𝐑𝐊𝐈

𝙔𝙖𝙣𝙙𝙖 𝙢𝙖𝙯𝙖𝙣𝙗𝙖𝙩𝙖 𝙠𝙚 𝙩𝙨𝙞𝙣𝙩𝙖𝙧 𝙠𝙬𝙖𝙧𝙤𝙧𝙤𝙣 𝙧𝙤𝙗𝙖 𝙨𝙪𝙣𝙖 𝙨𝙖𝙮𝙚𝙧𝙬𝙖 𝙟𝙖𝙢𝙖 𝙖