Zaɓen Edo: shin ankawo ƙarshen siyasar ubangida a Nigeriya?
Nasarar da Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya samu a zaɓen da aka gudanar a ƙarshen mako ta bijiro da ayar tambaya: Shin an kawo ƙarshen siyasar ubangida a Najeriya?
Wannan tambaya tana da matuƙar muhimmanci ganin cewa an kwashe shekara da shekaru ana siyasar ubangida, wadda masana harkokin siyasa suke ganin ita ce take tarnaƙi game da gudanar da mulki na gari a ƙasar.
Shi dai Mista Obaseki na jam'iyyar PDP, wanda Hukumar zaɓen ƙasar ta INEC ta bayyana cewa ya samu ƙuri'u 307, 955, ya doke Mista Osagie Ize-Iyamu na jam'iyyar APC wanda ya samu ƙuri'u 223,619.
Amma ba a nan batun siyasar ubangidan yake ba. An zaɓi Gwamna Obaseki a matsayin gwamnan jihar ne a ƙarƙashin jam'iyyar APC a 2016, kuma tsohon gwamnan jihar Adams Oshiomhole ne ya yi ruwa ya yi tsaki wajen gani nan zaɓe shi.
Sai dai wani rikici da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa tsakanin Mr Oshiomhole, wanda tsohon shugaban jam'iyyar APC ne na ƙasa, da Mista Obaseki, ya sa jam'iyyar ta APC ta hana gwamnan sake tsayawa takara a ƙarƙashinta.
Hakan ne ya sa gwamna ya sauya sheƙa zuwa babbar jam'iyyar hamayya ta Najeriya, PDP, wadda ta tsayar da shi takara.
A wani abu da masu lura da siyasa suke gani a matsayin arashi, jam'iyyar APC ta tsayar da Mista Osagie Ize-Iyamu, wanda shi ne mutumin da Gwamna Obaseki ya kayar a zaɓen gwamna a 2016 lokacin yana jam'iyyar PDP, a matayin ɗan takararta.
Sai dai tun kafin zaɓen, an yi ittifaƙi cewa za a yi fafatawar ce tsakanin Gwamnn Obaseki wanda ke son tabbatar da ƴancinsa na mutum mai zaman kansa, da kuma Mista Adams Oshiomhole, wanda ke son nuna masa cewa shi ne jigon siyasa a jihar ta Edo.
Gayyar ƴan siyasa
Yaƙin neman zaben ya yi zafi sosai inda aka riƙa musayar yawu tsakanin ɓangarorin biyu.
Baya ga haka, wasu jiga-jigan jam'iyyun biyu daga wasu jihohi daban sun ari rigar jihar sun yafa inda suka riƙa yi wa 'yan takarar jam'iyyunsu yaƙin neman zaɓe.
Misali, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano da tsohon gwamnan jihar Rabi'u Musa Kwankwaso sun farfaɗo da gabar da ke tsakaninsu a lokaci zaɓen na jihar Edo.
Fitattun ƴan siyasar biyu sun tafi jihar domin kowanne ya nuna irin ikon da yake da shi a siyasance.
Kazalika hamshaƙin ɗan siyasar nan na kudu maso yammacin Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar Lagos Bola Tinubu da wasu manyan ƴan APC sun tsoma kansu a siyasar ta Edo.
Hasalima Tinubu ya caccaki Gwamna Obaseki bisa salon shugabancinsa inda ya ce dole a kawar da shi idan ana son ci gaban jihar.
Tawayen masu kaɗa kuri'a
Sai dai masana harkokin siyasa na ganin kayen da APC ta sha a zaɓen Edo wata alama ce da ke nuna cewa 'yan jihar da ma wasu ƴan Najeriya sun dawo daga rakiyar jam'iyyar, wacce ake gani ba ta kawo sauyin da ta yi iƙirarin za ta kawo ba idan aka zaɓe ta.
Wani masanin siyasa Dr Sa'idu Dukawa ya ce ba ƙaramin ganganci gwamnatin Shugaba Buhari ta yi ba wajen ƙara kuɗaɗen man fetur da hasken wutar lantarki da kuma kayan abinci a wannan lokaci da take fuskantar zaɓen jihar.
A cewarsa, mazauna jihar Edo da wasu ƴan Najeriya sun ji raɗaɗin waɗannan ƙare-ƙare kuma zaɓen tamkar amsa ce ga jam'iyyar APC cewa ba su gamsu da irin mulkinta ba.
A nasa ɓangaren, Malam Kabiru Sa'idu Sufi na Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a da ke jihar Kano, ya ce kayen da APC ta sha a Edo tamkar jaddada aniyarta ce ta ƙyamar siyasar ubangida.
"Wannan ba shi ne na farko da 'yan jihar Edo ƙi siyasar ubangida ba. A baya shi kansa Oshiomhole ya kayar da su Tony Anenih lokacin suna ganiyarsu a wani salo na ban mamaki.
Za a iya cewa 'yan Edo ba sa son siyasar ubangida da ma can," in ji Malam Sufi.
Comments
Post a Comment