Posts

๐’๐ข๐ฒ๐š๐ฌ๐š๐ซ ๐š๐ฌ๐š๐ฅ๐ข๐ง ๐๐š๐ก๐š๐ฎ๐ฌ๐ก๐ž ๐›๐š๐ฆ๐š๐ ๐ฎ๐ฃ๐ž

Image
 ๐’๐ข๐ฒ๐š๐ฌ๐š๐ซ ๐š๐ฌ๐š๐ฅ๐ข๐ง ๐๐š๐ก๐š๐ฎ๐ฌ๐ก๐ž ๐๐š๐ฆ๐š๐ ๐ฎ๐ฃ๐ž:โ„Ž๐‘Ÿ๐‘ก๐‘ฃ๐‘›๐‘’๐‘ก๐‘ค๐‘œ๐‘Ÿ๐‘˜.๐‘›๐‘”@๐‘”๐‘š๐‘Ž๐‘–๐‘™.๐‘๐‘œ๐‘š ๐ท๐‘œ๐‘š๐‘–๐‘› ๐‘Ž๐‘–๐‘˜๐‘œ ๐‘š๐‘Ž๐‘›๐‘Ž ๐‘‘๐‘Ž ๐‘ โ„Ž๐‘Ž๐‘ค๐‘Ž๐‘Ÿ๐‘Ž ๐‘˜๐‘œ ๐‘Ÿ๐‘Žโ„Ž๐‘œ๐‘ก๐‘Ž๐‘›๐‘›๐‘–. Wata shekara, aiki ya kaini wata jiha a cikin jihohin arewa maso gabas. Da yamma sai na fito daga otel ษ—in da aka yi mana masauki, da nufin zagawa inga gari. Ko ba komi, ai Hausawa sun ce na zaune bai ga gari ba. A cikin gari nayi isha'i, sa'annan na fara tattaki da nufin dawowa masauki. A bisa hanya na hango wani shagon abinci irin wanda Turawa ke kira restaurant. Sai na faษ—a da nufin yin ฦ™oto. Bayan na zauna, an kawo mani irin abincin da na buฦ™ata har na fara ci, sa'annan ne na ankara da hirar da wasu matasa suke yi a wani teburin da ke cikin ษ—akin abincin. Matashi na Farko: Kakana, wanda ya daษ—e a cikin hausawa, shine ya ke tabbatar mani da cewa babu wasu mutane da ake kira hausawa. Duk wanda kaji ance bahaushe ne, to in ka bincika yana da asali a wata ฦ™abilar cikin kakanninsa. Matashi na Biyu:...

MAZAUNA KANO SUN KOKA BISA YAWAITAR SACE-SACEN GARIN TUWO

Image
   M  azauna Kano Sun Koka Bisa Yawaitar Sace-Sacen Garin Tuwo a Wajen Mas Mazauna Unguwannin Kurna, Dandishe da  Gobirawa dake Karamar hukumar Dala ta jihar Kano sun koka bisa yawaitar satar garin tuwo a wajen masu nika a jihar. Jaridar PRIME TIME NEWS ta rawaito cewa mazauna unguwannin sun yi korafin yawan bacewar gari a wajen nika a yan kwanakin nan, wanda hakan ya haifar da damuwa tsakanin mutane, musamman ganin yadda tattalin arzikin kasarnan ke cikin mawuyacin hali.  Haka kuma rahotannin sun bayyana cewa yawancin wadanda lamarin ya shafa, masu karamin karfi ne wadanda baza su iya siyan shinkafa ba sai dai su ci abin da ya shafi gari musamman masara da gero, wanda dole ne a nika shi kafin a sarrafa shi. Haka kuma, wannan jaridar ta gano cewa mazauna wasu yankuna a kwaryar birnin jihar Kano a yan kwanakin nan suna fuskantar yawan satar Gari a wajen masu nika, wanda hakan ya tilasta musu kula da abincin na su. Mamman Sani, wanda ke yin nika a Gobirawa, Kurna ya bayyana cewa...