Dubun Wata Shedaniyar Dorinar Ruwa Ya Cika Jihar Kebbi.
Dubun Wata Dorinar Ruwa Ya Cika A Jihar Kebbi.
Daga Wakilinmu.
Dubun wata dorinar ruwar da ta dade tana yin 6arna a garin sa-ma-na-ji da ke karamar hukumar Koko/Bessen jihar Kebbi ya cika,inda Mutanen garin suka yi nasarar zakulota a cikin ruwa suka kuma hallata barzahu.
Kafin samun nasarar kashe wannan Dabbar ruwan,kamar yadda rahotanni suka bayyana,ta dade tana yi wa al'ummar wannan gari mummunar 6arna ta hanyar hallaka masu Dabbobi,lalata gonaki har ma da salwantar masu da rayukan jama'a,inda daga karshe dai mutanen yankin suka fusata suka yi wa kududdufin da take ciki kawanya suka kuma hallakata har lahira bayan shafe tsawon yini guda cur suna artabu da ita.
Barnar da aka tabbatar Dorinar ruwan ta ta6a yi wa mutanen garin ya hada da; nitsar da jirgin ruwa har sau hudu,lalata gonakin shinkafa har ma da rasa rayukan mutane.
Jim kadan da samun wannan nasara ta kashe wannan dabbar ruwan,shugaban karamar hukumar Koko/Besse, Honarabul Yahaya Bello Koko,mataimakinsa Honarabul Umar Musa Besse,Uban kasar Dutsin Mari Alhaji Mu'allade da Kansilar Magaji,Manu Sule Koko da dai sauran al'ummar yankin sun yi tururuwa a bakin ga6ar kududdufi domin kashe kwalkwatar idonsu tare da Murnar nasarar kashe wannan Dabba da ta dade tana yi masu ta'adi.

Comments
Post a Comment