Wata Budurwa Ta Shirya Za6en Wanda Za Ta Aura Tsakaninta Samarinta A Bauchi.
Khadija: Budurwar Da Ta Shirya zaben Fidda Gwanin Da Za Ta Aura A Tsakanin Samarinta.
Wani abu kamar al'amara da ya faru a Karamar hukumar Giade ta Jihar Bauchin Tarayyar Najeriya,wata Budurwa ta shirya wa Samarinta biyu Za6en fidda gwani da zummar auren duk wanda ya lashe Za6en.
Budurwar mai suna Khadija tana da samari biyu; Inusa da Ibrahim dukkansu suna neman aurenta ita ma tana sonsu,amma sai dai ta kasa za6en daya Tilo bisa ra'ayinta domin ta aura, sakamakon yadda kwarjininsu ya dabaibayeta har sai da ta kai ga shirya za6en fidda gwani a tsakaninsu,za6en da Jama'ar kowanensu suka gabatar.
Bayan samarin sun yi yawon Campaigh(yakin neman za6e) a cikin maza6arsa,sai aka shirya za6e inda magoya bayan kowanensu ya bi layi ya kada Kuri'arsa,za6en wanda Manyan anguwa suka yi alkalancinsa.
Bayan tattara sakamakon za6e,an bayyana Inusa a matsayin wanda ya lashe za6en inda abokin hamayyarsa Ibrahim ya sha kaye ya kuma rungumi kaddara.
Tuni dai an ba wa Inusa 'Certificate' din shaidar da za ta ba shi damar ci gaba da zuwa tadi wajen Khadija,kafin zuwa lokacin da za a sa baikon aurensu.
A ganinku da haka 'yan mata ke shirya za6e a tsakanin samarinsu,anya da yawan fadace-fadace da ake samu tsakanin masu neman aurensu bai ragu ba kuwa?

Comments
Post a Comment