Maganin Korona Bairus A Iran: Kasashe Na Ta Rokon Iran Da Ta Taimaka Masu Da Shi.
Bayan fitar a rahoton kungiyar lafiya ta duniya (WHO) kan Iran,abokan aikin ministan harkokin kasashen wajen Iran,Muhammad Jawad Zarif sun yi ta bugo masa waya domin neman hadin kan Iran kan yakar cutar Corona bairus,tare da jinjina wa Iran din.
Da farko ministan harkokin wajen kasar Norway Mr.Marie Eriksen Sorede ne ya bugo waya, yana mai tunatar da Zarif din game da yarjejeniya Oslo wanda Iran da kasar suka sanya wa hannu cewar za su hada kai wajen taimakawa junansu kan lamurra daban-daban,ciki kuwa har da sha'anin kiwon lafiya.
Daga nan kuma sai na kasar Switzerland Mr,Ignazio Cassis ya bugo waya yana mai tambayar halin da ake ciki a Iran din game da cutar ta Corona. Sannan suka tattauna yadda sauran kasashen duniya ke ciki game da cutar,da kuma matakan ci gaban da ita Iran din ta samu wajen yakar cutar.
Daga nan kuma ministan harkokin wajen kasar Austria Mr.Alexander Schallenberg ya bugo waya yana taya Iran murnan samun cigaba wajen yakar wannan cutar,tare da kira ga Iran din wajen bai wa kasar gudummuwar kariya daga cutar.
Daga nan kuma sai ministan harkokin kasashen waje na Pakistan, Shah Manhood Quraishi ya bugo waya yana jajanta wa Iran, tare da neman hadin kan Iran wajen sha'anin kiwon lafiya.Sannaan kuma suka tattauna kan lanarin siyasar kasar Pakistan da kuma cigaban da aka samu a kasar Afghanistan ta fuskar zaman lafiya.
Daga nan kuma sai suka tattauna tare da ministan harkokin wajen kasar Rasha Mr.Sergei Lavrov kan halin da ake ciki a Syria game da mamayar da Turkiyya ke yiwa yankin Idlib. Haka kuma sun tattauna kan yadda za'a samar da zaman lafiya a yankin na Idlib da Syria baki daya.A karshe ya yaba wa Iran bisa jajircewarta wajen yakar cutar Corona.
A karshe Zarif ya tattauna da jagoran gudanar da harkokin siyasar yankin Turai baki daya Chief Joseph Borrel kan lamarin cutar Corona a Iran da duniya baki daya,sannan sai suka tattauna game da yarjejeniyar Nukiliya ta JCPOA.MR.Borrel ya yi wa Iran fatan alheri tare da jinjina mata wajen yakar cutar Corona.

Comments
Post a Comment