TSAWA DA RUGUGI A BIRNIN RIYADH

Nasir Isa Ali
Mazauna birnin Riyadh sun shiga zaman zullumi bayan sun ji kara da rugugin fashewar wani abun fashewa.
-
Bayan rundunar tsaron birnin Riyadh ta bayyana cewar,ta samu sa'ar kado wani makami mai linzami wanda yan Huthy suka harbo kan birnin a cikin daren lahadi,sai ga wata kara da rugugi ya afku kan birnin na Riyadh. Gidan TV din Al-Arabiyya ya bayyana cewar, rundunar tsaron Samaniyar Saudiya sun karkado wasu makamai biyu wanda aka harbo daga Yemen zuwa kan Riyadh da Jizan.
Haka zalika tashar El-Akhbariyya ta bayyana cewar, rundunar tsaron Saudiya sun kado wani makami mai cin nisan zango (Ballistic-Missile) a sararin samaniyar birnin Riyadh.
-
Amma kamfanin dillancin labaran AFP ya bayyana cewar,wakilansa sun jiyo wasu karar farfashewa da rugugi mai karfi a birnin na Riyadh. Su ma kansu mazauna birnin na Riyadh sun bayyana cewar sun jiyo kara da fashewar wasu abubuwa,tare da jin rugugi,daga baya kuma suka jiyo jiniya ! Alamar kowa ya zauna a inda yake.
-
Har yanzu babu wanda ya fito ya dauki nauyin wannan harin akan Riyadh,amma kwanan nan an jiyo shugabannin kasar Yemen suna yin gargadi ga Saudiya da Imarat da su daina kawo hare hare kan Yemen din ko kuma su fuskanci martani mai gauni.
-
Wani mazaunin Riyadh wanda yaki bayyana sunansa,ya bayyana bacin ransa kan Jagorancin Saudiyar ganin yadda suke jefa rayuwar yan kasar cikin hatsari saboda biyan bukatun Israila da Amurka.

Comments

Popular posts from this blog

JIRGIN RUWAN ANNABI NUHU DA AMURIKA TA KERA A SHEKARAR 2018

๐๐ˆ๐†๐„๐‘๐ˆ๐€ @60:๐Œ๐”๐‹๐Š๐ˆ๐ ๐’๐Ž๐‰๐€ ๐Œ๐€๐’๐” ๐‡๐€๐‹๐ˆ๐ ๐“๐’๐ˆ๐˜๐€ ๐ƒ๐€ ๐๐€ ๐Š๐ˆ๐‘๐Š๐ˆ

๐™”๐™–๐™ฃ๐™™๐™– ๐™ข๐™–๐™ฏ๐™–๐™ฃ๐™—๐™–๐™ฉ๐™– ๐™ ๐™š ๐™ฉ๐™จ๐™ž๐™ฃ๐™ฉ๐™–๐™ง ๐™ ๐™ฌ๐™–๐™ง๐™ค๐™ง๐™ค๐™ฃ ๐™ง๐™ค๐™—๐™– ๐™จ๐™ช๐™ฃ๐™– ๐™จ๐™–๐™ฎ๐™š๐™ง๐™ฌ๐™– ๐™Ÿ๐™–๐™ข๐™– ๐™–