CORONAVIRUS: Allah buwayi gagara misali.
COVID-19: KARFIN MULKIN ALLAH YA KARA BAYYANA A ZAHIRI...
A yanzu kasa mafi karfin soja a Duniya, tare da karfin tattalin arziki, wacce take ganin kamar ta gagari komai da kowa, ta zama abar tausayi, ta rikice tana ta neman tallafi daga ko ina sakamakon annoba guda daya kacal data ziyarcesu,
Yau dukkan manya manyan Hotels dake Las Vegas sun kasance a kulle, guraren Chacha dake les Vegas suna kulle, layukan dake kasar Amsterdam inda ake gudanar da karuwanci mafi tsada a duniya duk an rufesu, duk da makudan kudaden da ake samu har sama da 10 Billion Dollars a shekara, an wayi gari a duniya kowacce kasa ta rufe Night Clubs da guraren shan giya tare da guraren da ake taruwa domin aikata masha'a lallai Allah da karfi yake...
Da karfin ikon Allah yau kusan dukkan jiragen sama suna kasa a ajiye, an dena amfani dasu sakamakon tsoron annobar Coronavirus, shi kansa Shugaba Trump na amurka da bakinsa yake bayyana cewa kasarsa zata dakatar da karbar kudin ruwa don a samu sauki a halin da ake ciki,
Da karfin mulkin Allah yau Shugaba Putin na Rasha ya mayar da hankali wajen tattaunawa da shugaba Bashar na kasar Syria don ganin an dakatar da yakin da aka shafe shekaru anayi a kasar Syria duk saboda annobar Coronavirus hakan ke faruwa...
Yau a duniya dole ta sanya an koma amfani da mayafin rufe fuska kamar dai yadda ake saka Hijabi, duk domin kaucewa haduwa da annobar Coronavirus...
Cikin sati biyu kacal, an rasa sama da Dollars Trillion Goma sha shida duk saboda bayyanar Coronavirus...
Duniya ta rikice duk an bazama neman maganin Coronavirus, mutanen da a baya suke ganin kamar sun isa suyi duk abun da suke so saboda ilmin sanin dan adam da rayuwar duniya da suke dashi, yanzu sun gaza sun kasa samun maganin Corona, ina masu jiji dakai da suke ganin kamar sun isa, ina wadanda basu amince da samuwar Allah ba, kowa yayi shiru ya koma gefe yana ta fatan samun maganin Coronavirus...
Allah da girma yake, ikonsa ya mamaye ko ina a duniya, duk abun da akeyi kyalewa yayi, a yanzu da wasu suke ganin kamar zasu iya kirkirar mutum nasu na kansu, sai gashi Ubangiji ya saukar da yar kamarar lalurar data gagari kowa da komi a duniya...
Ikon Allah da mulkin Allah kadai sune na gaskiya da basa karewa, buwaya da daukaka duka suna wajen Ubangiji, cikin rahamarsa ne ya kyale Yan adam suke aikata abun da sukeso, ba wai don sun gagareshi ba....
Rubutun Fadakarwa ne daga Kamfanin Mudassir And Brothers, Chiarman Alhaji Mudassir Idris na adduar Allah ya kawar da annobar Coronavirus daga Nigeria da duniya gaba daya

Comments
Post a Comment