Saudiyya: Yarima Bin Salman Na Tsaka Mai Wuya.
Rikici A Saudiyya: Ana Zargin Yarima Muhammad Bin Salma da Kame-Kamen 'Yaya Da Jikokin Manya A Masarautar Saudiyya.
Rikici tsakanin 'yaya da jikokin Ahli Sa'ud yana ta kara kamari a masarautar a 'yan kwanakin nan inda Rundunar kare masarautar Saudiyar ta kara cafke wasu 'yayan gidan su Uku ciki kuwa har da wasu manyan yarimomi biyu.
Rahotannin da ke fitowa daga masarautar na tabbatar da cewar,da sanyin safiyar yau Asabar ne aka cafke Yarima Ahmad bin Abdulazee shakikin sarkin Saudiya na yanzu (Salman bin Abdulazeez) da kuma yarima Muhammad bin Nayef kamar yadda mujallar "Wall Street Journal" ta ruwaito.
Ana kyautata zaton cewar,ayyanannen yariman Saudiya Muhammad bin Salman da mahaifinsa suna da hannu dumu-dumu wajen wannan kitimurmura ta Kamesu.
Jaridar "The New York Times" ta habarto labarin kuma ta kara da cewar,ita ma ta samu rahoton cewar,an kama dan uwan yarima Nayif wato Nawaf bin Nayef.
Ya kawowa yanzu dai, hukumomi a masarautar sun tsuke bakinsu kan wannan badakalar.
Wannan dai shi ne wani sabon kamu akan wasu kame-kamen da aka yi a baya wanda ake zargin Yarima Muhammad bin Salmam (MBS) na yi wa yarimomin domin gyara wa kansa kar6ar ragamar masarautar cikin sauki,ganin mahaifin nasa (Sarki Salmanu) na dada kusantar kushewarsa.
Shi dai yariman Saudiya (MBS) yana kakkame duk masu kalubalantar manufofinsa a Saudiya,wadanda ake ganin sun yi hannun riga da musulunci da ala'adu na Kasar Saudiyyar.Haka zalika, ana yawan kashe masu adawa da shi a ciki da wajen kasar ta Saudiyya.
In za a iya tunawa ko a watan Okutobar shekarar 2018 kamar yadda rahotanni suka tabbatar, yariman ya tura aka halaka wani dan jarida mai adawa da shi wato Jamal Kasshoggi a ofishin jakadanci Saudiya da ke a Istanbul na Kasar Turkiyya.

Comments
Post a Comment