Posts

MUHIMMAN ABUBUWA BIYAR DA BUHARI YAYI MAGANA A KANSU-bbc hausa

Image
Nigeria @60: Muhimman abubuwa biyar da Buhari ya ce yayin jawabinsa Sa'o'i 5 da suka wuce ASALIN HOTON, NIGERIA PRESIDENCY A ranar Alhamis, 1 ga watan Oktoban 2020 ne Najeriya ta cika shekara 60 da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka. A safiyar Alhamis ne shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya yi jawabi na musamman ga 'yan ƙasar inda jawabin ya fi mayar da hankali kan haɗin kan ƙasar. Ga wasu daga cikin muhimman batutuwan da shugaban ya taɓo a jawabinsa: Haɗin kai Jigo ko kuma babban saƙo a cikin jawabin shugaban ƙasar shi ne kan batun haɗin kai, domin shugaban a wurare daban-daban ya nuna cewa idan 'yan ƙasar suka haɗa kansu za a samu ci gaba mai ɗorewa. "Idan muka haɗa kanmu za mu iya sauya yadda muke a yanzu domin kawo ci gaba mai amfani a garemu kuma za mu iya taimakon kanmu ƙwarai". Shugaba Buhari ya bayyana cewa ta hanyar haɗin kai ne 'yan Najeriya za su magance ƙalubale daban-daban da suke fuskanta Warkar da Najeriya daga raunin da ta samu...

𝐒𝐢𝐲𝐚𝐬𝐚𝐫 𝐚𝐬𝐚𝐥𝐢𝐧 𝐁𝐚𝐡𝐚𝐮𝐬𝐡𝐞 𝐛𝐚𝐦𝐚𝐠𝐮𝐣𝐞

Image
 𝐒𝐢𝐲𝐚𝐬𝐚𝐫 𝐚𝐬𝐚𝐥𝐢𝐧 𝐁𝐚𝐡𝐚𝐮𝐬𝐡𝐞 𝐁𝐚𝐦𝐚𝐠𝐮𝐣𝐞:ℎ𝑟𝑡𝑣𝑛𝑒𝑡𝑤𝑜𝑟𝑘.𝑛𝑔@𝑔𝑚𝑎𝑖𝑙.𝑐𝑜𝑚 𝐷𝑜𝑚𝑖𝑛 𝑎𝑖𝑘𝑜 𝑚𝑎𝑛𝑎 𝑑𝑎 𝑠ℎ𝑎𝑤𝑎𝑟𝑎 𝑘𝑜 𝑟𝑎ℎ𝑜𝑡𝑎𝑛𝑛𝑖. Wata shekara, aiki ya kaini wata jiha a cikin jihohin arewa maso gabas. Da yamma sai na fito daga otel ɗin da aka yi mana masauki, da nufin zagawa inga gari. Ko ba komi, ai Hausawa sun ce na zaune bai ga gari ba. A cikin gari nayi isha'i, sa'annan na fara tattaki da nufin dawowa masauki. A bisa hanya na hango wani shagon abinci irin wanda Turawa ke kira restaurant. Sai na faɗa da nufin yin ƙoto. Bayan na zauna, an kawo mani irin abincin da na buƙata har na fara ci, sa'annan ne na ankara da hirar da wasu matasa suke yi a wani teburin da ke cikin ɗakin abincin. Matashi na Farko: Kakana, wanda ya daɗe a cikin hausawa, shine ya ke tabbatar mani da cewa babu wasu mutane da ake kira hausawa. Duk wanda kaji ance bahaushe ne, to in ka bincika yana da asali a wata ƙabilar cikin kakanninsa. Matashi na Biyu:...

MAZAUNA KANO SUN KOKA BISA YAWAITAR SACE-SACEN GARIN TUWO

Image
   M  azauna Kano Sun Koka Bisa Yawaitar Sace-Sacen Garin Tuwo a Wajen Mas Mazauna Unguwannin Kurna, Dandishe da  Gobirawa dake Karamar hukumar Dala ta jihar Kano sun koka bisa yawaitar satar garin tuwo a wajen masu nika a jihar. Jaridar PRIME TIME NEWS ta rawaito cewa mazauna unguwannin sun yi korafin yawan bacewar gari a wajen nika a yan kwanakin nan, wanda hakan ya haifar da damuwa tsakanin mutane, musamman ganin yadda tattalin arzikin kasarnan ke cikin mawuyacin hali.  Haka kuma rahotannin sun bayyana cewa yawancin wadanda lamarin ya shafa, masu karamin karfi ne wadanda baza su iya siyan shinkafa ba sai dai su ci abin da ya shafi gari musamman masara da gero, wanda dole ne a nika shi kafin a sarrafa shi. Haka kuma, wannan jaridar ta gano cewa mazauna wasu yankuna a kwaryar birnin jihar Kano a yan kwanakin nan suna fuskantar yawan satar Gari a wajen masu nika, wanda hakan ya tilasta musu kula da abincin na su. Mamman Sani, wanda ke yin nika a Gobirawa, Kurna ya bayyana cewa...