JIRGIN RUWAN ANNABI NUHU DA AMURIKA TA KERA A SHEKARAR 2018
Amurka 'ta kera jirgin Annabi Nuhu' 2 Nuwamba 2018 Wanda aka sabunta 8 Nuwamba 2018 An sabunta labarin bayan da aka fara wallafa shi ranar 20 ga watan Yulin 2016. ASALIN HOTON, GETTY IMAGES Bayanan hoto, An kashe Dala miliyan 100 wajen gina jirgin Ma'aikatar kirkire-kirkire ta jihar Kentucky ta Amurka, ta kashe tsabar kudi har Dala miliyan 100 wajen gina wani jirgin ruwa kwatankwacin kwamin Annabi Nuhu, bisa dogaro da yadda aka siffanta shi a littafin Injila. Kelly Grovier ya yi nazari kan hakan. Shin da me kake neman tsira a wannan duniyar? Addini? Ko Iyalinka? Ko kuma harkar wasanni? Wasu hotuna da suka rinka kai-komo a kafafen yada labarai da na shafukan sada zumunta, a 'yan kwanakin nan dangane da wani jirgin ruwa da aka gina, sun haddasa wata mahawara a tsakanin mutane a arewacin jihar Kentucky, abin da kuma ya yi nuni da irin yadda al'umma ke neman kariya daga wasu bakin al'adu da ba sa so. Hotunan katafaren jirgin da aka gina domin kwaikwayon kwamin Annab...